Maulidin Annabi Farillane, Murna Da ‘Yancin Kai Sunnace Ta ‘Yan Nijeriya ~ A Cewar Young Sheikh

Maulidin Annabi Farillane, Murna Da ‘Yancin Kai Sunnace Ta ‘Yan Nijeriya ~ A Cewar Young Sheikh

 

Fitaccen malamin nan mai karamin Shekaru wato Young Sheikh haifaffen garin Zariya Jihar Kaduna, ya kawo wasu hujjo inda yace Maulidin Annabi Muhammadu (S.A.W.) farillace, bisani nuna Farin ciki da samuwar ‘Yancin Kai a Nijeriya wannan Kuma Sunnace ta ‘Yan Nijeriya.

 

A cikin jawabinnasa yace! Idan Kayi Murnan Samun Yanci Daga Bautan Turawa Kayi Sunnah.

 

Murnan Samun Annabi Muhammadu Wanda Yasamar Maka da Yancin Rashin Bautan Wanin Allah Wannan Farillah Ne.

 

Muna Taya Yan Nigeria Murnar Zagayowar Ranar Samun Yancin Kai Daga Mulkin Turawan Mulkin Mallaka.

 

Kamar Yanda Shehu Ibrahim Yace;-

 

عَلَيْــــــهِ صَـــلاَةُ اللّٰهِ ثُـــمَّ سَلاَمُـــــهُ

وَيَحْفَظُ لِي دِينِي وَقَوْمِي كَذَا الْوَطَنْ

Su Tabbata A Gareshi (Annabi Muhammad ﷺ) Salatin Allah Sannan Amincin Sa, Sababin Sa Ya Kiyaye Min Addini Na Da Jama’a Da Kuna Qasa Ta.

 

وَدَوْلَتُهُ سِنْغَالُ فِي إِفْرِقَيَا

وَعَاصِمَةٌ لِلْفَيْضِ كَانُو نِيجِيرِيَا

Qasar Sa Itace Senegal A Cikin Africa, Kuma Babban Birnin Faira Shine Kano A Nigeria.

 

وَنِيجَرْ بِهَا أَفْرَادُ قَوْمٍ مَقَامُهُمْ

بِمَنزِلَةِ الْوَزَرَا كَمَا فِي نِيجِيرِيَا

A Niger Akwai Dai-daikun Mutane Wadanda Maqamin Su Suna Kan Kujerar Shuwagabanni Kamar Yadda Yake A Nijeriya.

 

A karshe Shehin Malamin ya yiwa Kasa addu’a, da fatan Allah Yakarawa Kasarmu Nijeriya Zaman Lafiya da Arziki Mai Amfani.

Share

Back to top button