MAULUDI UMARNIN ALLAH(S.W.T) NE. Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

MAULUDI UMARNIN ALLAH(S.W.T) NE

 

MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

 

“Idan Ka Ji Mutum Yana Sukar MAULUDI, To Ka Ce Masa; Ai MAULUDI Iri Biyu(02) Ne:

 

*. Akwai MAULUDI Na Zamani Wato Watan RABIUL AWWAL, A Watan Bature Kuma a APRIL, Wannan Shi Ne MAULUDI Na Zamani,

 

Akwai Kuma MAULUDI Na Makani(Wuri) Wato MAKKAH Da MADINA,

 

SHEHU(R.A) Ya Ci Gaba Da Cewa; Idan Mutum Ya Samu Kudin Zuwa Hajji Zai Tafi Dolensa, Shin Anan Waye Ya ‘Kra Shi???

 

Aka Ce; ALLAH(S.W.T),

 

Don Haka Duk Wanda Ya Tafi MAKKAH Da MADINA, To Ya Tafi MAULUDIN MANZON ALLAH(S.A.W) Ne Na Makani,

 

Zai Je Ya Ga Inda Aka Haifi ANNABI (S.A.W),

Ya Ga MasallacinSA, Ya Ga GidanSA, Ya Ga Ababen Da ANNABI(S.A.W) Yayi Rayuwa Da Su,

 

Don Haka Kenan Dole Ne Musulmi Yayi MAULUDI, Ko Na Makani Wato Zuwa MAKKAH Da MADINA, Ko Na Zamani ‘Din Wato Watan RABIUL AWWAL Ko APRIL, ALLAH Ya Barmu Da Son ANNABI (S.A.W)”.

 

ALLAH Ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH DAHIRU (R.A). AMIIIN

Share

Back to top button