Mauludin Annabi Muhammadu SAW Umurnin Allah Ne, Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

MAULUDI UMARNIN ALLAH (S.W.T) NE

 

MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

 

“Idan Ka Ji Mutum Yana Sukar MAULUDI, To Ka Ce Masa; Ai MAULUDI Iri Biyu(02) Ne:

 

*. Akwai MAULUDI Na Zamani Wato Watan RABIUL AWWAL, A Watan Bature Kuma a APRIL, Wannan Shi Ne MAULUDI Na Zamani,

 

Akwai Kuma MAULUDI Na Makani(Wuri) Wato MAKKAH Da MADINA,

 

SHEHU(R.A) Ya Ci Gaba Da Cewa; Idan Mutum Ya Samu Kudin Zuwa Hajji Zai Tafi Dolensa, Shin Anan Waye Ya ‘Kra Shi???

 

Aka Ce; ALLAH(S.W.T),

 

Don Haka Duk Wanda Ya Tafi MAKKAH Da MADINA, To Ya Tafi MAULUDIN MANZON ALLAH(S.A.W) Ne Na Makani,

 

Zai Je Ya Ga Inda Aka Haifi ANNABI(S.A.W),

Ya Ga MasallacinSA,

Ya Ga GidanSA,

Ya Ga Ababen Da ANNABI(S.A.W) Yayi Rayuwa Da Su,

 

Don Haka Kenan Dole Ne Musulmi Yayi MAULUDI, Ko Na Makani Wato Zuwa MAKKAH Da MADINA, Ko Na Zamani ‘Din Wato Watan RABIUL AWWAL Ko APRIL, ALLAH Ya Barmu Da Son ANNABI(S.A.W)”.

 

Allahumma Ameeeen

 

ALLAH Ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH(R.A). Amiin

Share

Back to top button