Mu Tashi Mu Nemi Dukiya (Halal). Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

MU TASHI MU NEMI DUKIYA (Ta Halal);

 

LISANUL-FAIDHA (Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A) Yana Cewa:

 

“ALLAH (S.W.T) Cikin Hikimarsa Da Ya Tashi Tura Da’awa Zuwa Ga SAYYIDA BILKISU Sai Aka Tura Mata ANNABI SULAIMAN(A.S),

 

Dalili Saboda Tana Tinkaho Da Dukiya Da Mulki, Sai ALLAH Ya Za6i Wanda Yake Da Ita(Dukiyar) Fiye Da Ita Cikin Annabawansa,

 

Da ANNABI ISA(A.S) Aka Tura Mata, Da An Samu Tangarda Saboda Shi Irin Mu’ujizarsa Ba Zata Yi Aiki Anan Ba, Domin Shi Ko ‘Dakin Kwana Ma Baya Da Shi,

 

Haka ALLAH Yake Tsara Lamarinsa”.

 

ALLAH Ya ‘Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH(R.A). Amiin

Share

Back to top button