Muhimman Abubuwan Da Malamai Suka Bayyana Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Wata Ziyara.
Malamin addinin Musulunci, sun yiwa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari nasiha a ziyarar da suka kai masa a kwanakin baya.
Sannan sun ja hankalinsa kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi al’ummar Arewacin ƙasar nan.
1 Malaman sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an Allah ya bashi ikon kammala mulki lafiya.
2 Sun sake tunatar dashi nauyi da yake kan sa na al’ummar Najeriya.
3 Mun bashi shawarwari akan abubuwan da suke faruwa a kasa don ya gyara kuma ya dauki mataki.
An tattauna maganar manyan ayyuka da gwamnatin tarayya take yi wanda ya kunshi titin dogo daga Kano zuwa kasar Niger da kuma titin mota daga Kano zuwa Kaduna, zuwa Borno.
An tattauna maganar man fetur da aka haku a jihar Gombe/Bauchi wanda malamai suka bada shawara akan ayi kokari wurin kammala wannan muhimmin aiki wanda zai amfani arewacin Najeriya.
Anyi magana akan bankuna na Bank of Industry da kuma bank of Empowerment wanda basa bawa yan arewacin Najeriya bashi kudi, kuma ya kamata a karfafa bangaren bankuna Musulunci kamar Ja’iz, da Jaz da sauran wanda yan arewacin Najeriya zasu amfana.
Daukacin malaman sun bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sharawa akan a cigaba da inganta fanni tsaro da tattanin arziki a arewacin Najeriya tare da taimakawa mutane.
Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yada da wannan ziyara inda ya bayyana cewa malamai ba neman kudi ko mulki bale ya kawo su wurin mai mulki ba, ya kuma gode masu da irin wannan shawara da tunatar wa.
Allah ya amfanar damu cikin wakilcin malaman Addinin Islama ya bashi ikon kariya sauran ayyuka masu amfani ga Najeriya. Amiiiin