MUHIMMAN NASARORI GUDA 10 DA YA CIMMA KASA DA SHEKARU 10

MUHIMMAN NASARORI GUDA 10 DA YA CIMMA KASA DA SHEKARU 10.

 

Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H).

 

1-RAGE TSAURIN AKIDANCI DA ZAZZAFAR KIYAYYA TSAKANIN MUSULMI:- Ko ayayin da da’awarsa ta daukaku da budeddiyyar tunani, ankararwarsa ta fadada akan illa da kuma hatsarin MUSULMI ya kira, ko nasabta kalmar KAFIRCI ga dan uwansa MUSULMI, sannu a hankali sashen Musulmin da suka sunnata hakan, suma abin ya soma zama kauyanci garesu, karshe dai sun takaita kafirta Musulmin da ba dan kungiyarsu ba.

 

2- KOYAR DA SUNNAH A AIKACE:- Kunnuwa sun saba jin Malami ya dage da ikirarin koyar da sunnah a karance, tare da siffatuwa da sunnah a sutura ko a barin gemu, amma karshe sai ka samu ayyukansa sunyi hannun riga da koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W) a ma’amalance, A kasa da Shekaru 10, ya zamo daya cikin Jagororin da suka raya Sunnah a aikace, domin hatta ‘Yan Kungiya ko idan suka mu’amalceshi, karshe sukan bada shaidar tsananin amanarsa, gaskiyarsa, kirkinsa, zuhudunsa, da kuma kyautatawarsa wanda dayawa daga Malamansu basu rabauta da samun hakan ba.

 

3- YADA KARANTARWAR ADDINI ZUWA LUNGUNA DA SAKON KAUYUKA:- Ya dauko wani yunkuri a wasu lokuta da suka gabata, na kafa Makaranta guda, a kowanne Sati, cikin daya daga Kauyuka a kauyukan Arewancin Nigeria, inda akan dauki Maluma suna shiga Lunguna suna koyar da al’umma yadda ake ibada da sauransu, domin rage tsananin Jahilcin da yake haifar da matsalar tsaro a yankuna arewancin Kasarnan.

 

4- ZABURARWA DA KOKARIN CICCIBA MATASA GA NEMAN ILMI MAI ZURFI NA ADDINI DA NA ZAMANI :- Bazaka iya kirga adadin wadanda suka taki matakai masu zurfi ba ta wannan fanni, inda wasu suka zamo Daktoci ayayin da wasu suka samu shaidar Masters bisa zaburarwarsa.

 

5- FITO DA SABBIN FATAWOWI BISA DACEWA DA ZAMANIN DA MUKE CIKI :- Domin saukaka samar da amsoshi ga dimbin kalubai da zamani yazo dasu, da ake bukatar fatawowi akai, yayi rubuce-rubuce tare da bayar da fatawowi domin samar da amsoshi akan hakan, inda Musulmi suka samu waraka daga shakku akan dimbin abubuwa dake cike da shubha.

 

6- TAFSIRI TA HANYAR BAYAR DA AMSA GA YAKIN SUNKURUN ORIENTALIST DA SCIENTIST AKAN KALUBALANTAR KUR’ANI DA YAKAR MUSULUNCI A ILMANCE:- Tafsirinsa cike suke da bincike mai zurfi wajen samar da dimbin amsoshi masu saita tunani, wajen yin martani ga kalubalen da wadancan ja’irai keyi, inda ya zamo silar ‘yanto dimbin matasa daga zama Mulhidai, bayaga fidar ganin har hanji da yakeyiwa duk mas’ala muhimmiya da ya taras.

 

7- KIRA TARE DA AIKI DOMIN KARFAFAR HADIN KAN MUSULMI:- Zaka samu karantarwarsa cike yake da kira da kuma kwadaitarwa akan abin da zai haifar da maslaha da hadinkai tsakanin Musulmi, wanda dalilin hakan ya samar da wata gidauniya ta “QAFILATUL MAHABBAH” domin kira akan hakan, bayan samun Izini daga Maulana Shareef.

 

8- SAMAR DA MAKARANTU DOMIN KARANTAR DA MASU KARAMIN KARFI, DA KUMA MAKARANTUN ZAMANI:- Ya assasa Makarantun Jillul Jadeed a wasu daga garuruwa, inda ake karantar da ‘ya’yan Musulmi Ilmomin Addini tun daga matakin Farko har zuwa matakin Kololuwa, inda a gefe guda kuma ya samar da Makarantun Zamani masu matukar zubi da tsari, Kamar Mahrajal Bahrain, duk domin samar da gobe mai kyau ga matasa.

 

9- TALLAFAWA DA AGAZAWA RAUNANA DA MARAYU:- baya ga manufar hadin kan Musulmi, hakanan gidauniyar da ya assasa ta “QAFILATUL MAHABBAH” na aiki matuka, wajen kokarin taimakawa Marayu, Gajiyayyu da masu karamin Karfi a kusan Ilahirin Jahohin dake Arewancin Nigeria.

 

10- FADADA MAULUDI, DAGA SHIRYA TARO KADAI, ZUWA MAULUDIN ZUWA ASIBITTOCI, DA GIDAJEN GYARAN HALI ANA TALLAFAWA MARASA LAFIYA, DA DAURARRU.

 

Wadannan kadanne daga tarin nasarorin da ya cimma, wanda kowanne guda cikinsu idan akace za’a fadada bayani akai, to karkashinsa za’aci karo da wasu tarin nasarorin da bazasu lissafu ba. Yakai ga hakanne sakamakon juriyarsa ga dimbin cutarwa, hakurinsa da kuma matukar himma da kokarinsa.

 

FATANMU, ALLAH YA KARA MASA LAFIYA, KUSANCI, JURIYA DA HAKURIN HIDIMAR AL’UMMAR MANZON ALLAH (S.A.W).

 

Daga: Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button