Muna Allah Wadai Da Rattaba Hannu Da Yan’majalisun Nigeria Suka Yi Na Tsarin SAMOA.

KIRA GA SHUGABANNI DA YAN’ MAJALISAR TARAYYAN NIGERIA.

 

Mu duka musulmin Nigeria muna Allah wadai da rattaba hanu da gwamnatin tarayya tayi akan yarjejeniyar SAMOA, wanda zai sahhale dokar Madigo da kare hakkin yan Luwadi a Nigeria.

 

Gwamnati ta yarda da yarjejeniyar ne saboda makudan kudi da suka kai Dala Billion 150 da bankin duniya zai baiwa Nigeria a matsayin tallafi.

 

Hakika Bamu yarda kasarmu mai Addini da Al ãda a maida ta ballagazar ‘kasa kamar sauran kasashen turai ba, duk wani wakilin mu a majalisa da ya yarda da wannan mummunan kudiri, toh yasan yaci amanar Allah yaci amanar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم kuma yaci amanar al ummar da yake wakilta, kuma wallahi lahirar sa bazatayi kyau ba dan ya riga yayi cinikin ta tun a duniya

 

Allah ya daukaka musulunci ya karya kafirci ya daukaka gaskia yakarya karya ya karya masu yiwa addini zagon ’kasa a Nigeria Albarkan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.

 

Imam Hassan Sheikh Dahiru Bauchi

Share

Back to top button