Musulman Najeriya Yan Tijaniyya sune mafiya rinjaye sama da mutum Miliyan 50 mabiya Darikan Tijaniyya a Najeriya.

KUNDIN TARIHIN TIJANIYYA

 

TAKAITACEN TARIHIN SHIGOWAN DARIKAR TIJJANIYYA A NIJERIYA

 

Tarihin yaduwar Tijjaniyya a Nijeriya yana komawa ga mutane uku wadanda suka dauki dawainiyar yada darikar. Wadan nan mutane su ne, Shaihu Maulud Fal, Shaihu Umar Alfuti da Shehu Sharif Muhammad wanda aka fi sani da lakabin Sharu Zangina.

 

• Shaihu Maulud Fal ya kasance daga cikin manyan ‘yan Tijjaniyya wadanda suka yi aiki sosai wajen yada darikar, musamman a arewaci da yammacin Afirka. Shi mutumin Muritaniya ne, amma ya yi tafiye-tafiye da dama. Ya wuce ta Kasar Hausa a kan hanyarsa ta zuwa aikin Hajji inda ya shigar da Modibbo Ahmadu Raje cikin darikar. Ahmadu Raje shi ne kakan galadiman Adamawa Muhammadu, kuma ijazar (takardar izinin shiga darikar) da Shaihu Fal ya rubuta masa da hannunsa har yau tana nan a adane a wurin zuri’ar Galadiman Adamawa.

 

•Shehu Umar Alfuti babban dan Tijjaniyya ne wanda a sakamakon kokarinsa darikar ta samu kafuwa a dukkan sassan Afrika ta yamma. Umar Alfuti ya karbi darikar daga hannun Shaihu Abdulkarim Nakil wanda shi kuma tun da farko ya karbo ta daga Shaihu Maulud Fal, wanda muka gabatar da ambatonsa. Umar Alfuti ya zo kasar nan a zamanin Sarkin Musulmi Muahmmad Bello dan Shehu. Ya zauna a Sakkwato na wani lokaci, ya auri diyar Sarkin Musulmi Bello, sa’an nan ya wuce zuwa Makka inda ya game da shugaban Tijjaniyya na wannan zamani, Shaihu Muhammad Gali, wanda ya nada shi mukaddami a darikar. A kan hanyarsa ta komowa daga Hajji, Umar Alfuti ya biyo ta garuruwan Kukawa, Bauchi, Zaria, Katsina da Kano. A ko wane gari ya sauka, ya kan yi kokari ya nema wa darikar magoya baya. Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Muhammad Bello, Umar Alfuti ya koma garinsu, Futa Toro, wanda a yau yake cikin kasar Senegal.

 

• Shi kuwa Shaihu Zangina, wanda ake jin cewa yana daga cikin jikokin Shaihu Tijjani, ya kawo ziyara ne birnin Kano a zamanin Sarki Alu Maisango. Daga Kano ya wuce zuwa Zaria, kuma ya zarce har zuwa garin Lokoja a inda Allah ya yi masa rasuwa.

 

Banda wadan nan Shaihinnai uku, akwai mutane da dama wadanda suka zo kasar nan don aikin yada darikar Tijjaniyya kamar su Shaihu Muhammad binu Usman wanda ya zo daga Moroko, da Shaihu Abdulwahhab wanda aka fi sani da lakabin ‘Sharif Ujudud’. Sai dai a cikin dukkan wadan nan Shaihinnai tasirin Sharu Zangina shi ya fi karfi; domin daga wajensa ne Shaihin da ya yada Tijjaniyya a yawancin biranen arewacin Nijeriya, watau Shaihu Muhammad Salga, ya karbi darikar. Daga cikin wadanda suka karbi darikar a hannun Shaihu Muhammadu Salga akwai Malam Ahmadu daga Gwandu, Malam Dangoggo daga Sakkwato, Malam Hassan Kafunga daga Kano, Malam Abba daga Damagaran, Malam Hassan daga Kwantagora, Malam Ibrahim Mai Rigar Fata daga Borno, da sauransu.

 

Bayan tsawon lokaci da yaduwan Darikan Tijaniyya a Arewacin Najeriya sai daga bisani Dariqar ta shiga kudancin Najeriya ta hannun Muhammad Wali, mutumin Ilorin. Daga bayan shi ne Alfa Salih Abdulkadir ya kai dariqar Tijjaniyya Ibadan, lokacin da ya je Ilorin.

 

Dariqar Tijjaniyya ta samu a Ijebu+Ode (Ogun State) a karni na Ashirin (20) ta hanyar ‘yan uwa kamar: Imam Hassan Amokeoja (D. 1920) da Alfa Alawaiye (D 1928).

 

A yanzu haka a cikin Musulman Najeriya mabiya Darikan Tijaniyya sune mafiya rinjaye domin a kalla za’a iya samun sama da mutum Miliyan 50 mabiya Darikan Tijaniyya a Najeriya.

 

Insha Allahu a karkashin wannan maudu’i na Kundin Tarihin Tijaniyya zamu rinka Kawo muku Tarihin Shehunnan Tijaniyya da irin gudunmawa da suka bawa Musulunci da Darika da Faidha baki daya, sai a ci gaba da binmu.

 

A karshe muna rokon Allah ya sakawa Shehunnan mu da Alkhairi wadanda sukayi dawainiyar yada wannan Alkhairi har ya zo gare mu. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button