Mutumin Da Ya Zagi ANNABi Muhammadu SAW Cikin Wani Littafin Da Ya Rubuta Wani Ya Daba Masa Wuta.

Wani Mutum Ya Dabawa Salman Rushdie Wuka, Mutumin Da Ya Zagi ANNABI Cikin Wani Littafin Da Ya Rubuta.

 

An kai wa marubucin nan Salman Rushdie, wanda aka kwashe shekaru da dama ana yi wa barazanar kisa bayan ya rubuta littafin da ya ci zarafin Addinin Musulunci mai suna “Ayoyin Shedan” The Satanic Verses), hari.

 

An kai masa harin ne yayin da yake jawabi a wurin wani taro a Jihar New York da ke Amurka.

 

Marubucin, wanda ya lashe kyautar The Booker Prize, yana jawabi ne a Cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa hari.

 

Ganau sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi inda ya rika naushi yana kuma daba wa Mr Rushdie wuka a yayin da ake gabatar da shi gaban jama’a.

 

Daga BBC Hausa.

Share

Back to top button