Na Lura Duk Wata Halitta Ta Yi MAULUDI, Ba Ma Ga ‘Yan Adam Ba Kawai. Inji Sheikh Ibrahim Inyass RA.

MAULANMU SHEHU IBRAHIM ABDULLAHI NIASSE(R.A) Yana Cewa:

 

“NI Na Lura Duk Wata Halitta Ta Yi MAULUDI, Ba Ma Ga ‘Yan Adam Ba Kawai, Domin;

 

*. Katangar Kisra Ta Yi Mauludi Inda Ta Rarrawa Ta Tsage Saboda Haihuwar MANZON ALLAH(S.A.W).

 

*. Wutar Farisa Ta Yi Mauludi, Shekara Dubu Ana Hura Ta Amma a Lokacin HaihuwarSA(S.A.W) Ta Mace.

 

*. ‘Koramar Buhairata Sawata Ta ‘Kafe Saboda HaihuwarSA(S.A.W), Alhali Ana Zaton Ba Za Ta Ta6a ‘Kafewa Ba.

 

*. ‘Koramar Dabariyya Ita Ma Ta Yi Mauludi Inda Ta Kawo Ruwa a Lokacin HaihuwarSA(S.A.W), Alhali Ta Yi Shekaru Masu Yawa a ‘Kafe.

 

*. Taurari Sun Yi Mauludi Inda Suka Sauko ‘Kasa-‘Kasa a Daren HaihuwarSA(S.A.W).

 

*. Karagogin Manyan Sarakunan Duniya Sun Yi Mauludi Inda Suka Kife Saboda Haihuwarsa(S.A.W)”.

 

ALLAH YA ‘KARA MANA ‘KAUNAR MA’AIKI(S.A.W), YA ‘KARA MANA HIMMA CIKIN HIDIMAR SHUGABA(S.A.W) AMEEEEEEN.

Share

Back to top button