Na rantse muku da Allah duk wadda kuka ga ya soki Shehu Dahiru a yau wallahi da ya zo lokacin Shehu Ibrahim sai ya soke shi,
A Hankalce ! Kaf muridan Shehu Ibrahim wadanda mutane suka sani Babu wadda ya gaje shi ta fuskoki da yawa irin Maulana Sheikh.
1: Ta fuskar saɓawa da kowa a kan bin gaskiya.
2: Ta fuskar sabanin fahimta da ƴan uwansa a Dariqar Tijjaniya hatta zuri’ar Shehu Tijjani.
3: Ta fuskar tsagwaran maƙiya hatta ƴan Tijjaniya.
4: Ta fuskar tarin mabiya masu rauni a duniyance da masu wadata.
5: Ta fuskar tarin ƴaƴa.
6: Ta fuskar yawan tafiye-tafiye dan yaɗa Shari’a da Dariqa.
7: Ta fuskar samun ƙarfafaffiyar alaƙa da dukkan waliyan Allah.
8: Ta fuskar samun galaba akan dukkan maƙiyi na ciki da na waje.
9: Ta fuskar yawan karatun Alqur’ani da sanin fiqhunsa.
10: Ta fuskar yafiya da ƙaunar halitta.
11: Ta fuskar jamala da jalala.
12: Ta fuskar ƙaunar almajiran Shehu Tijjani da tsayuwa kan damuwarsu.
13: Ta fuskar yawan zuwa aikin hajji da umara da ziyarar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
Na rantse muku da Allah duk wadda kuka ga ya soki Shehu Dahiru a yau wallahi da ya zo lokacin Shehu Ibrahim sai ya soke shi, domin yau babu wata nasama da take irin aikin Gausi fiye da Shehu dahiru a doron ƙasa, idan kuma akwai ta to a zo mana da maziyarta…..
Ahmad Muhammad Dahir
At-tijaniy Al-hanifiy
Abul Abbas
17 – jul – 22