Najeriya ta fi kowace ƙasa yawan mahaddata Alkur’ani a duniya – Sheikh Dahiru Bauchi RA.

Najeriya ta fi kowace ƙasa yawan mahaddata Alkur’ani a duniya – Sheikh Dahiru Bauchi

 

Shehun malamin ya ce Najeriya ta sha bamban da sauran kasashe wajen haddar Alkur’ani.

 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Shugabanin Darikar Tijjaniya na Afirka, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce Najeriya ta fi kowace kasa yawan mahadatta Alkur’ani mai girma a fadin duniya.”

 

Ya ce a fadin duniya babu kasar da ta kai Najeriya yawan mahaddata Alkur’ani wanda hakan, ya sa kasar ta zama daban da sauran kasashe.”

 

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wajen bikin yaye dalibai mahaddata da gidauniyarsa ta Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta gudanar, karo na hudu a Gombe.”

 

Shehun malamin ya samu wakilcin ɗansa, Sayyadi Ali Shiekh Dahiru Bauchi, inda ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta tsananta a Najeriya.”

 

Ya kuma gargadi mahaddatan da cewa Alkur’ani, ba abun wasa ba ne, inda ya jaddada bukatar kada su yi wasa da shi.

 

Kazalika, ya yabawa masu yi wa addinin Musulunci hidima don ganin ya samu daukaka a Najeriya da ma duniya baki daya.”

 

Sai dai ya ja hankalin masu hannu da shuni da su rungumi akidar taimakawa marasa karfi don rage musu radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta.”

 

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya samu wakilcin Kwamishinan Kimiyya da Kere-Kere, Farfesa Abdullahi Bappah Garkuwa.

 

Kwamishinan ya jinjina wa Sheikh Dahiru Bauchi, kan kafa gidauniyar a jihohin kasar nan, wanda hakan ke kara yawan mahaddata Alkur’ani.

Back to top button