Ni Bani Da Wani Ɗan Takara Ɗaya Tak Da Zan Zaba. Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR

PRESS RELEASE;

 

Zantawar MAULANMU SHEHU TAHIRU (R.A) Da ‘Yan Jaridu a Jiya Litinin 20-02-2023

 

“INA SON KOWA YA FITA YA ZAƁI WANDA YAKE SO, DON NI BA NI DA WANI ƊAN TAKARA” – SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI.

 

Babban Shehun Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shehu Ɗahiru Usman Bauchi Ya Ce; Ba Shi Da Wani Ɗan Takara Ɗaya Tak Da Zai Ce a Zaɓa a Babban Zaɓen Shugaban Ƙasa a Najeriya Da Za a Gudanar a Ranar Asabar Mai Zuwa.

 

Shehu Ɗahiru Usman Bauchi Wanda Ya Ke Amsa Tambayoyi Daga Manema Labaru a Abuja Ya Ce; Shi Kowa Na Sa Ne a ‘Yan Takarar, Don Haka Ya Ke Bukatar Jama’a Su Yi Amfani Da Hankalinsu Wajen Zabar Wanda Su Ka Ga Ya Dace a Babban Zaɓen.

 

Kazalika Malamin Ya Yi Fatan Duk Wanda Ya Lashe Zaɓen Ya Zama Sabon Shugaban Najeriya To Ya Mai Da Hankali Wajen Kawo Hanyoyin Da Talakawa Za Su Samu Sauƙi Daga Ƙuncin Tattalin Arzikin Da Ake Fama.

 

“Gwamnatin Nan Da Mu Ka Fito, Ba Mu Ji Daɗin Ta Ba, Akwai Abubuwa Da Yawa Na Matsuwar Mutane a Zamaninta, Wanda Ba Mu Ji Daɗinsu Ba, Kamar Tsare(Rufe) Ƙasa a Hana Komai Shiga, Na Ciki Kuma Ba Ya Isa, Mu Ne Talakawa ‘Yan Ƙasa Ba Mu Ji Daɗin Waɗannan Ba.”

 

Malamin Ya Gabatar Da Addu’ar Zaman Lafiya Mai Ɗorewa a Najeriya Ya Na Mai Yabawa Manema Labaru Da Yanda Su Ke Aikin Isar Da Saƙonnin Wayar Da Kan Jama’a.

 

(©️Mai Rahoto/Rubutawa; Nasiru Adamu El-Hikaya, VOA Hausa).

 

Ameeeen, Ameeen SHEHU(R.A).

 

ALLAH Ya Kara Maka Lafiya Da Nisan Kwana, Ya Sa Mu Kammala Waɗannan Zaɓuka Da Muka Saka a Gaba Lafiya, Ya Bamu Mafi Alkhairi, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W) Amiiiin

 

Daga: Othman Muhammad

Share

Back to top button