Niyya shine mutum ya fadi a sirrance a zuciyar sa cewa yana nufin aiwatar da wani aiki na ibada ga Allah.
MU KOYI NIYYAR IBADA
Niyya shine mutum ya fadi a sirrance a zuciyar sa cewa yana nufin aiwatar da wani aiki na ibada ga Allah. Niyya wajibi ne cikin kowani ibada, in babu niyya, aikin ibada ba zai karbu ba. Ga wasu muhimman niyyoyi wayanda muke aiwatar da ayyukan su kullum ko akai-akai.
NIYYAR ALWALLA.
Niyya biyu ake yi yayin alwalla. Da farko in zaka wanke tafin hannu zuwa wuyan hannu sannan kuskure baki sannan shaqar ruwa a hanci, sai ka fara yin wannan niyyar “BISMILLAHI NAWAITU SUNANUL WUDU’I”. Idan kazo wanke fuska kuma sai kace “NAWAITU FARA’IDAL WUDU’I” sannan ka cigaba da alwalla har ka gama.
NIYYAR SALLOLIN FARILLA
(kai kadai ko a jam’i ko kuma ramuwa).
1. ASUBA: NAWAITU ADÃ’A SALATIS SUB-HI FARDAN.
2. AZAHAR: NAWAITU ADÃ’A SALATIZ ZUH-RI FARDAN.
3. LA’ASAR: NAWAITU ADÃ’A SALATIL ASRI FARDAN.
4. MAGARIBA: NAWAITU ADÃ’A SALATIL MAG-RIBI FARDAN.
5. ISHA’I: NAWAITU ADÃ’A SALATIL ISHA’I FARDAN.
Toh idan sallar Qada’i (ramuwa) ce, sai ka cire ADÃ’A da kake fadi a niyyar sallar da ba ramuwa ba, kace misali “NAWAITU QADÃ’A SALATIZ ZUH-RI FARDAN” idan sallar azahar ce.
Toh idan kuma zakayi salla a jam’i, wato za ka bi liman, sai ka qara IQTIDÃ’A BIL IMAM a gaban kowacce niyya, ko a sallar ramuwa ko wacce ba ramuwa ba. Ga misali:
Sallar Asuba wacce ba ramuwa ba kuma a jam’i, sai kace NAWAITU ADÃ’A SALATIS SUB-HI FARDAN IQTIDA’A BIL IMAM. Idan kuma sallar ramuwa ce a jam’i, sai kace NAWAITU QADÃ’A SALATIS SUB-HI FARDAN IQTIDÃ’A BIL IMAM.
NIYYAR SALLAR JUMA’A
Ita dai dama mutum daya baya yin ta, kuma in ka rasata sai dai kayi azahar, don haka niyyar ta daya ce kamar haka “NAWAITU ADÃ’A SALATIL JUMU’ATI FARDAN IQTIDÃ’A BIL IMAM”.
NIYYAR LAZUMI, WAZIFA DA ZIKIRIN JUMA’A
1. LAZUMIN SAFE: ALLAHUMMA INNIY NAWAITU AN ATAQARRUBA ILAIKA BI WIRDIS-SABÃHIL LAZUMI FI DARIQATIT TIJJANIYATI IQTIDÃ’A BI SHEIKHANA AHMADU TIJJANI RADIYALLAHU TA’ALA ANHU.
2. LAZUMIN YAMMA: ALLAHUMMA INNIY NAWAITU AN ATAQARRUBA ILAIKA BI WIRDIL MASÃ’IL LAZUMI FI DARIQATIT TIJJANIYATI IQTIDÃ’A BI SHEIKHANA AHMADU TIJJANI RADIYALLAHU TA’ALA ANHU.
3. NIYYAR WAZIFA: ALLAHUMMA INNIY NAWAITU AN ATAQARRUBA ILAIKA BI QIRÃ’ATIL WAZIFATI FI DARIQATIT TIJJANIYATI IQTIDÃ’A BI SHEIKHANA AHMADU TIJJANI RADIYALLAHU TA’ALA ANHU.
4. ZIKIRIN JUMA’A
ALLAHUMMA INNIY NAWAITU AN ATAQARRUBA ILAIKA BI TILAWATI ZIKIRIL HAILALATIL JUMU’ATI FI DARIQATIT TIJJANIYATI IQTIDÃ’A BI SHEIKHANA AHMADU TIJJANI RADIYALLAHU TA’ALA ANHU.
Wazifa da zikirin juma’a, Shehu Tijjani ne limamin ka direct ba muqaddamin dake zaune tare da kai a jam’i ba, shiyasa aka ambace shi kai tsaye.
Zikirin juma’a ba a ramawa in lokacin ta ya wuce, kuma ko kai kadai zakayi, niyyar da zakayi kenan. Amma Idan za ka rama lazumi ko wazifa, a jam’i kake ko kai kadai, za ka fadi QADA’A a cikin kowacce niyya kamar misali lazumin safe, dama shi lazumi ba a yin sa a jam’i, sai kace
ALLAHUMMA INNIY NAWAITU AN ATAQARRUBA ILAIKA BI QADA’A WIRDIS-SABÃHIL LAZUMI FI DARIQATIT TIJJANIYATI IQTIDÃ’A BI SHEIKHANA AHMADU TIJJANI RADIYALLAHU TA’ALA ANHU.
✍ Sidi Sadauki