Prof. yace a dai duba littafin da kyau tukun kafin ace wai ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) bai san gaibu ba.

SHIN MANZON ALLAH (S.A.W) YASAN GAIBU?

 

Prof. Ibrahim Maqari. Limamin masallacin kasa dake abuja (Chief imam national mosque) – Nigeria

 

Prof. Yace Adai duba littafin da kyau tukun kafin ace wai ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) bai san gaibu ba

 

Prof. Ibrahim Maqary yace idan mutum yace maka ANNABI S.A.W bai san gaibu ba, Kar kace masa Wallahi Tallahi ANNABI S.A.W yasan gaibu bazaku fahimci juna ba.

 

Abunda zakayi sai ka tambaye shi menene

gaibu? Idan mai ilimi ne zai ce maka Allah Qaibu ne Sai ka tambaye shi

 

“toh Allah ne ANNABIN bai sani ba” ??

 

Zai sake ce maka mala’iku qaibu ne, sai kace masa ai

 

“Mala’ikun yan aiken sa ne. Ai aiken su ya keyi S.A.W”

 

Ba ANNABI S.A.W ba, wanda ma ya zauna

kusa dashi sai ya gansu. Su Mala’ikun kuma Zai sake ce maka Aljanna da wuta Qaibu ne Sai kace masa

 

“Ai Ana zaune a duniya Manzon Allah ke zuwa ya dawo har yace yaga wane kaza acikin wuta kuma yaga wane kaza acikin aljannah”

 

“Ana zaune zai ce ga Aljanna ga wuta a gabana ku kuna ganin bango shi yana ganin Aljanna”

 

Zai sake ce maka abunda zai faru nan gaba Qaibu ne! Sai kace masa

 

“A tsayuwa daya ANNABIN ya bada labarin abinda zai faru har tashin Alqiyama”

 

“KANA FEENA RASULULLAHI S .A .W

MAQAMAN FAMA TARAKA SHA’IN TAKUUNU FI MAQAMA MIHI ZALIKA ILA QIYAMISSA’ATI ILLAH HADDASANA BIHI”

 

Allah yakarawa Professor lafiya da fahimta bijahi Rasulullalahi S.A.W. Ameen

Share

Back to top button