Professor Rudiger Seeseman Yana Daga Cikin Manyan Almajiran Sheikh Ibrahim Inyass A Duniya.
Baturen Dan Faidah Sheikh Ibrahim Inyass Wanda Ya Rubuta Littafi Akan Sahibul Faidati.
Wannan Baturen sunan sa Professor Rudiger Seesemann yana ɗaya daga cikin manyan turawa Almajiran Sheikh Ibrahim Niass Sahibul Faydha kuma jagora a ɗarikar Tijjaniyya.
Prof, Rudiger Seesemann ya rubuta wani fitaccen littafi da yai suna sosai a kasashen turawa mai sunan “The Divine Flood” ya rubuta shi akan rayuwar Sheikh Ibrahim Niass Al Khaulaha.
Rubutun da yai kan shehun malamin baƙar fata ne daga yankin Afirka dake kasar Senegal littafin ya ƙara fito da kimar mutanen Africa musulmai sosai manya manyan jami’o’i a ƙasashe daban-daban na turawa sunsha shirya taruka don karrama Shehun malamin kuma rubutun littafin yasan yawa turawa da yawa sun ƙara fahimtar cewa Musulunci Addini ne na zaman lafiya ba tashin hankali ba.
Professor Rudiger Seesemann haziƙin bature mai himma wurin cigaban Addinin Musulunci da kuma darikar Tijjaniyya.
Allah ya saka masa da alkhairi, ya kara mana irin su cikin al’ummar Manzon Allah SAW. Amiin
Daga: Khalid Ikara