RAHOTO: Ziyaran Sarkin Kano Dr Aminu Ado Bayero Kasar Algeria Tare Da Tawagar Sa.

CIKAKKEN RAHOTON: Ziyara Sarkin Kano Dr, Aminu Ado Bayero Da Alh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi Tare Da Tawagar Sa Kasar Algeria.

 

Daga Babangida Alhaji Maina

 

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Dr Aminu Ado Bayero ya ziyarci kasar Algeria da Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA don gabatar da wasu muhimman abubuwan a Algeria inda suka samu tarba na musamman daga babban Khalifan Tijjaniyya na duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi da Sidi Ahmad bin Sidi Abdel Jabbar da manyan jami’an gwammati an kuma shirya masa liyafar cin abincin rana domin karrama shi. Tare Da Yan tawagar sa.

 

Ziyaran wanda ta kunshi muhimman abubuwan masu muhimmmanci inda suka gabatar Algeria international conference mai taken Imam Mohammed Ibn AbdulKarim Al Maghili Governance Stability and Unity Of African Societies. A ranar 13/12/2022.

 

Bayan kammala taron tawagar mai martaba sarkin Kano Dr, Aminu Ado Bayero sun ziyarci garin Aina Madi inda aka haifi shugaban Darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Ahmed Tijjani RA, inda Khalifa Ali Bel Arabi ya bayyana cikakken tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA tare da tarihin gidan maulanmu Shehu Tijjani RA.

 

Tawagar mai martaba sarki da manyan shehunai da malamai tare da masu rakiya sun ziyarci masallacin Sidi Muhammad Al-Habib, mai cike da tarihin a Musulunci da Tijjaniyya.

 

A karshen ziyarar mai martaba sarki, ita ce kabarin Sidi Belarabi El Damraoui, inda aka karanta Fatiha na littafin don hadiya gare shi da sauran al’ummar Musulmai baki daga, wanda Sheikh Sidi Belmashri ya Jagoranci.

 

Babban bako mai martaba sarkin ya nuna matukar jin dadinsa da wannan ziyara da ya zama wajibi ga kowane dan Tijjaniyya ya kasance matakin farko a darikar sa shine Sheikh Sharif Ahmadu Tijjani RA, da kuma matsayin darikar Tijjaniyya a tsakanin bangarori da dama na ‘yan Najeriya. An kuma gabatar wa da mai martaba sarkin Kano sakon girmamawa wanda ya dace da matsayin da na basarake mai daraja.

 

Cikin tawagar akwai Sheikh Prof, Muhammad Kabir Yusuf Hamdani, Dr Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Dr, Lawi Sheikh Atiku Sanka, Ambassador Munir Yusuf Liman, Sayyadi Muktar Ibrahim Dahiru Bauchi.da sauran su.

 

Allah ya dawo mana dasu gida lafiya, ya bada ladan ziyara, Allah ya kara taimako. Amiiiin

Share

Back to top button