Ranar Juma’a Za’a Gudanar Da Jana’izan Sayyid Hassan Nasrallah Ya Yi Shahada Yana Da Shekaru 64 a Duniya,

A gobe Juma’a ne za a gudanar da sallar jana’izar Shahid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, kamar yadda kafar yada labaran kasar Iraki ta rawaito.

 

Kamfanin dillancin labarai na Sabrin ta wallafa wani rahoto da ya ambato wata majiya ta musamman da ba a bayyana sunanta ba a safiyar yau alhamis cewa za a gudanar da bikin jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah da aka kashe.

 

Wannan kafar yada labarai ba ta fayyace cikakken bayani game da lokacin jana’izar da kuma wurin da za a binne Shahidi Nasrallah da aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai kan wasu wuraren zama da ke wajen birnin Beirut a ranar Juma’ar da ta gabata.

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne jiragen yakin gwamnatin kasar Isra’ila su jefa bama-baman da suka kai fam 2,000 na Amurkawa a yankin Beirut mai yawan jama’a, inda suka kashe Nasrallah tare da wasu fararen hula da dama a can.

 

Sayyid Hasan Nasrallah ya yi shahada yana da shekaru 64 a duniya, sannan kuma bayan ya rike kungiyar Hizbullah a matsayin babban sakataren kungiyar na tsawon shekaru 32.

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button