RANAR MALAMAI: Sheikh Ibrahim Inyass Shine Shugaban Malaman Wannan Zamanin Karni Na 21.

RANAR MALAMAI NA DUNIYA

 

Na ga BBC Hausa sunyi sanarwa/ tunatarwa akan yau ne ranar malamai na duniya.

 

Ko za ku taya ni tuna wa duniya alherin da wannan bijimin waliyyin yayi wa addini da duniya baki daya?

 

Kun rasa ta ina zaku fara ko? Kuna iya farawa ta daya daga cikin wayannan 👇

 

1. Fannin hidimar sa ga Africa wurin kwatowa kasashen dake ciki yancin kai, musamman yan Nigeria wayanda da yawa basu san shehu yana sahun magabata na farko da suka yi fafatukar samun yancin qasar ba.

 

2. Fannin hidimar sa ga addini wurin kawo hadin kai tsakanin musulman duniya, har lambar yabo sai da ya samu a saudiya da sauran kasashe.

 

3. Fannin shaharar sa a duniyar ilimi tunda dai shine farkon wanda ya fara girgiza jami’ar azhar, wayanda suke bugun kirji suke “ko waye kai a duniyar ilimi, toh muna da irin ka anan guda 1000”, sai ga shehu yasa su kaffara.

 

4. Babu laifi in kuka tsakaro mana kararomin sa wayanda a kirge babu wanda yasan adadi nasu.

 

5. Kuna iya magana a kan almajiran sa wayanda suka zama dirka ga rumfar musulunci.

 

6. Kuna iya magana a inda yafi son a sosa masa, wato soyayyar sa ga Annabi SAW.

 

Yan’uwa bismillah cikin gausul waqati

 

#BayeNiass #Faida #islam

 

✍Sidi Sadauki

Share

Back to top button