RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA BIYAR (5).

RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA Part (5) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE

 

BAYANI AKAN TABBATAR DA KAMAWA WATA Part 2:

 

A wani Hadisin kuma da Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Wata kan yi kwana ashirin da tara. Kada ku kama Azumi har sai kun ga wata da qwayar idonku.

 

Idan kuma kuka kasa ganinsa saboda wani dalili, to ku bari sai Sha’abana ya cika kwana talatin.”

 

Saboda haka babu wani dalili da zai sa mutum ya dauki Azumi kafin a tabbatar da tsayuwar wata, wai don ko daka yi. Domin kuwa Shari’a ta riga ta yi wa al’amarin makama.

 

Saboda haka ne ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mana kashedi da “Ko daka yi” ya ce: “Kada ku kuskura ku kama Azumi tun watan Ramalana bai tsaya ba, ku bari sai an gan shi da qwayar ido, sannan, idan kuma an ga Sha’abana ta wannan hanya, ku aje. Idan kuma giragizai suka hana ku ganin sa, to, ku jira Sha’abana ya cika qwana talatin.

 

A wani Hadisi kuma ya ce: “Kada ku yi Azumin nafila da kwana daya ko biyu kafin watan Ramalana ya tsaya, sai fa wanda ke yin wani Azumi daban, shi kam irin wannan mutum ya samu ya yi Azuminsa.”

 

Ka ga a shar’ance abin da wadansu mutane ke yi wato Azumin “Ko daka yi” laifi ne. Saboda wadannan Hadissai da suka tabbatar da rashin halaccin fara Azumin Ramalana ba tare da an ga jinjirin watansa da qwayar ido, ko aka tabbatar da cikar Sha’abana kwana talatin ba,

 

Ammaru dan Yasir Raliyallahu Anhu ya ce: “Duk wanda ya yi Azumin “Ko-aka yi” haqiqa ya saba wa Baban Qasimu Sallallahu Alaihi Wasallama.

 

Amma kuma duk da haka, idan mutum bai san yadda ake kirdadon tabbatar da tsayuwar jinjirin wata ba, kuma ba ya da wanda zai isar masa a kan haka. Idan ya yi wannan Azumi na “ko-aka yi” amma da niyyar idan an yin, to, ya riga ya kimtsa. Idan kuma ba a yin ba, to, ya dauki Azumin nasa a matsayin nafila.

 

To, Azuminsa ya inganta a zance mafi rinjaye. Saboda niyya na tabbata ne a lokacin da masaniya ta tabbata, kuma hukuncinsu daya ne.

 

Idan har ya tabbata cewa watan na Ramalana ya tsaya, to wajibi ne ya yi wa Azumin nasa matsaya.

 

Da kuma a irin wannan hali zai yanke niyyar yin Azumin nafila ne, ko Azumi kawai, to, da sakal. Domin kuwa umurnin da Allah ya yi masa shi ne na daura niyyar yin Azumin Ramalana, wanda ya wajaba a kansa, wanda kuma idan ba shi ya yi ba, da sauran magana.

 

Amma idan ba ya da masaniya da cewa watan Azumi ya tsaya, to, ba wajibi ne a kansa ya yanke wa Azumin nasa hukunci ba.

 

Duk kuwa Malamin da ya wajabta yanke hukuncin a irin wannan hali, to kamar ya daura aure ne tsakanin ruwa da wuta.

 

Allah shi ne masani.

 

Yau da musulmi za su dawo su qanqame wannan Sunnah ta Manzo. Su tsaya a kan ganin qwayar ido ko cikar watan Sha’abana kwana talatin, don tabbatar da kamawar watan Azumi, da an huta.

 

Wata fitina ba za ta sake tashi ba, balle a yi ta jayayya a kan halaccin yiwuwar amfani da hisabi da ilimin zamani, ko rashin haka.

 

Domin kuwa a shar’ance ba ya hallata a qetare abin da nassi ya zo da shi. To, kuma ga shi abin da nassi ya qunsa a wannan al’amari, shi ne dogara a kan gani na qwayar ido, ba hisabi ba.

 

Amma kuma duk da haka, da za a yi amfani da na’aurorin zamani a tabbatar da haihuwar watan, sannan ya bayyana a fili a gan shi da ido, to, wajibi ne a yi aiki da hakan. Domin kuwa waccan magana ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ta batse hakan ba, balle. Don cewa ya yi “Kada ku dauki Azumi ko ku aje shi sai an ga jinjirin watansa da qwayar ido.

 

” Idan kuma hakan ta faskara, sai batun jiran kwanakin Sha’abana su ciki talatin, kamar yadda nassin ya tabbatar.

 

Kuma duk da haka, ba laifi ba ne a yi amfani da tabaran hangen nesa kamar kuma yadda yin hakan ba tilas ba ne. Saboda abin da Sunnah ta nuna qarara, shi ne dogara a kan gani irin na qwayar ido, kuma na al’ada kawai. Kuma shi ne kawai abin da ke wajaba a kan al’umma don tabbatar da bayyanar jinjirin wata. Allah shi ne mafi sani. Allah yasa muna fahimtar karatun

 

Allah ya karbi Ibadun mu na wannan watan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button