RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA BIYU (2).

RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA Part (2) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE

 

1.3 Yin Bushara ga Sahabbansa:

A duk lokacin da watan Azumi ke goshin kamawa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan tara Sahabbansa ya yi masu bushara da irin alhairan da watan ke dauke da su.

 

Yakan yi haka ne da nufin yi wa Sahabban nasa qaimi, don zaburar da su, su zare dantse, kowa ya kwashi rabonsa. Akwai Hadissai da dama da ke bayani a kan haka, ga kadan daga cikinsu:

 

Annabi S.A.W yakan ce masu: “Idan Watan Azumi ya kama, ana bude qofofin samu’u hayan-hayan, a kuma rufe qofofin Jahannama kaf, sannan kuma a daure Shaidanu.”

 

Yakan kuma ce: “Da zarar daren farko na Watan Azumi ya kama, sai a daure shaidanu a kuma ququnce aljannu, a rufe qofofin Wuta ba za a bude ko daya daga cikinsu ba, a kuma bude na Aljanna, ba za a rufe ko daya daga cikinsu ba.

 

Sai kuma wani mai shela ya yi kira ya ce: “Duk mai nufin alheri ya matso ga dama ta samu, duk kuma mai nufin sharri ya kama kansa. Kuma Allah ya yi alkawalin ‘yanta wasu bayi daga shiga Wuta, kowane dare.”

 

Yakan kuma gaya masu cewa:“Watan nan na Azumi mai abarka ya kama. Allah ya wajabta azuminsa a kanku. A cikinsa ne ake bude qofofin sama’u, a rufe na Jahimu, a kuma daure shaidanu. Haka kuma Allah na da wani dare a cikinsa wanda alfarmarsa ta fi ta wata dubu.

 

Duk wanda bai sami alherin da ke cikinsa ba, ya tabe har abada.” Yakan kuma gaya masu cewa: “Haqiqa a cikin Aljanna akwai wata qofa ana kiran ta Rayyanu, ta nan ne masu Azumi za su bi a ranar qiyama. Babu kuma wanda zai shige ta bayan su. Za a kira su ne daban ba tare da kowa ba, a bude masu ita, a kuma mayar a rufe har abada.”

 

Da wannan kuma muke kira da babbar murya, ga masu wa’azi da shugabannin musulmi, da cewa ya kamata su kula da wadannan Hadissai na bushara, su watsa su cikin duniyar Musulunci, don mutane su san girman Watan Azumi da irin falalar da yake tare da ita. Su kuma koya masu yadda za su ci moriyar wannan gajiya tasa.

 

Domin kuwa ta haka ne kawai farin cikin kamawar watan za ta zama hantsi leqa gidan kowa. Wanda za ta sa kowa ya shagaltu da neman masaniya da makamar ibadar. Ba kawai a taqaita ga shirya gara da daula ba, ta yadda har manufar Azumin za ta kasa tabbata ga mafi yawan mutane.

 

Allah ya sa mu dace, Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button