RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA DAYA (1).

RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA DAGA TASKAR UMAR CHOBBE

 

Wannan babi zai yi tsokaci ne a kan yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke kasancewa kafin watan Azumin Ramalana ya kama, ta hanyar yawaita Azumin nafila da yake yi a cikin watan Sha’abana, da yi wa Sahabbansa bushara da kamawar watan, tare da yi masu bayanin abubuwan da yake xauke da su na falala, da wasu abubuwa masu kama da haka.

 

1.1 Shimfida:

Kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mutum mai matuqar tsoron Allah Subhanahu Wa Ta’ala da gudun duniya, da tsananin kwadayin abin da Allah Ta’ala ya yi tanadi na kyakkyawan sakamako gobe qiyama. Sai hakan ta sa yake qara murna da farin ciki, a duk lokacin da wani yanayi na saukar alherin Allah da rahamarsa da jinqayinsa ke qara qamari.

 

Yana kuwa yin haka ne Sallallahu Alaihi Wasallama saboda cika umurnin AllahSubhanahu Wa Ta’ala da yake cewa: “Kace, su yi farin ciki da samun falalar Allah da rahamarsa. Wannan shi ne mafi alheri fiye da abin da suke Tarawa.” (10:58)

 

Wannan aya na tabbatar da cewa yin farin ciki da abin da Allah Ta’ala ya saukar a cikin Alqur’ani, ya kuma hori bayinsa da aikatawa, wanda ya haxa da abubuwa na wajibi da na mustahabbi, kamar Azumin Ramalana, wanda kusan babu wani wajibi da ya sha gabansa. To, yin farin ciki da samuwar waxannan abubuwa a falsafar Musulunci, shi ne mafi zama alheri, bisa ga duk wani farin ciki da bawa zai yi a kan tarin tulin wani abu na duniya.

 

Malam Sa’adi na cewa, qarin bayani a kan wannan aya: “Ko alama, ba a hada ni’imar addini da ta abin duniya; matsayinsu ba daya ba. Ni’imar addini ta hada arzikin duniya ne, da na lahira baki daya. A yayin da shi kuwa abin duniya, ko a duniyar ba ya da wani garanti. Domin kuwa gishirin qoqo ne, ana cikin kadi yake qarewa. Saboda haka ne Allah Ta’ala ya hori musulmi da yin farin ciki a kan samuwar falala da rahamarsa na addini. Domin hakan na lamunce masu kwanciyar hankali da nishadi da godiya ga Allah Ta’ala. Wanda a sakamakon haka sai su qara samun qwarin guiwa, da tsananin kwadayi da sha’awar ilmi da inganta imaninsu.

 

Wannan shi ne farin ciki na Shari’a. Ita kuwa murna a kan wani abu na sha’awoyin duniya da jin dadinta, ko natsuwa da faruwar wata masha’a, aikin banza ne. Domin kuwa Allah Ta’ala ya yi tir da masu yin annashawa don abin duniya. Kamar yadda yake ba mu labarin irin yadda ta kasance tsakanin Qaruna da mutanensa, inda suka ce masa; “Kada ka yi fahariya, lalle ne Allah ba ya son masu fahariya (da abin duniya).” (28:76)

 

Haka kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya yi wa wasu mutane kashedi da yin bugun gaba saboda wani abu da suka mallaka na barna, sabanin abin da Manzanni suka zo da shi na shiriya, inda yake cewa:“Sa’annan a lokacin da Manzanninsu suka je masu da hujjoji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi.” (40:83) wannan kenan.

 

Sannan kuma tabbataccen abu ne cewa, babu wani abu da ke gaggauta kusanta bawa da Ubangijinsa, da xaukaka alqadarinsa tare da lamunce masa yardar Mahalicci, da saka shi gaban sahu, kamar irin watan Azumin Ramalana da ire-irensa.

 

Matuqar bawa ya gudanar da ibadodi a cikin irin wadannan lokutta kamar yadda aka umurce shi, ta hanyar zare damtse da yin da’a ga Ubangijinsa, lalle ya rabauta.

 

Saboda haka ne Annabi S.A.W ba ya sake da irin wadannan lokuta. Da zarar an ce watan Azumin Ramalana ya gabato, to, sai Ma’aiki ya sha damara ya shirya ransa da zuciyarsa da gangar jikinsa, ta yadda zai fuskanci wannan ibada cikin cikakken nishadi. Wanda hakan za ta ba shi damar cin moriyar watan baki daya.

 

Muhimman hanyoyin da Annabi S.A.W ke taron Watan Azumi da su, sun hada da:

 

1.2 Yawaita Azumi a Cikin Watan Sha’abana:

 

Annabi S.A.W kan yawaita Azumin nafila a cikin wannan wata saboda fuskantar Watan Azumi.

 

Nana Aisha Raliyallahu Anha na cewa; Annabi S.A.W na yawaita Azumin, har mu yi zaton ba zai daina ba har abada. Wani lokacin kuma ya yi ta cin abincinsa, har sai mun zaci ba zai sake Azumin nafila ba har abada. Kuma ban taba ganin Manzon Allah S.A.W ya share wata daya cur yana Azumi kullum ba, in ba watan Ramalana ba. Ban kuma ga watan da yake yawaita Azumin nafila a cikinsa ba, bayan Ramalanan, kamar watan Sha’abana.”

 

A wata riwaya kuma aka ce, cewa ta yi:”… Ban taba ganin Annabi na Azumi da yawa a cikin wata daya ba, kamar yadda yake yi a cikin watan Sha’abana. Ina ganin ma yana azumtar sa ne baki daya.

 

Kai ko bai yi haka ba, ‘yan kwanukan da yake sha a cikinsa kadan ne.”

 

Saboda haka, a kan wannan Hadisi, abu ne mai kyau ga kowane musulmi, ya yawaita Azumi a cikin watan Sha’abana. Malamai sun ce: “Azumi a cikin watan Sha’abana kamar Sallolin nafila ne da aka sunnanta yi kafin na farilla. Share fage ne wato shi, wa Ramalana. Saboda haka aka sunnanta shi aka kuma sunnanta yin Azumin kwana shida a cikin watan Shawwal, kamar dai yadda ake yin nafilfili kafin da kuma bayan Sallar farilla.”

 

Amma duk da haka, mafi yawan mutane a yau sun yi ko-oho da wannan koyarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai wanda Allah ya taimaka. Alhali kuwa dubaiban mutane na iqirarin bajinta da kasancewa amale a cikin ruqumma. Wasu kuma suna tinqaho da kasancewa masu neman manya-manyan Sunnoni su qanqame, a matsayinsu na masu koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 

To, mu sani dabbaqa wannan Sunnah ta yawaita Azumi a cikin watan Sha’abana ne kawai zai sa mu ribanci alherin da ke cikin wannan wata mai albarka.

 

Allah ya yi mana mawafaqa Albarkan ANNABI S.A.W, amin. Allah yasa muna fahimtar karatun

 

Allah ya karbi Ibadun mu na wannan watan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button