RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA SHIDA (6).

RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA Part (6) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE).

 

Ita kuwa cewar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Azumi da idin qaramar Sallah da layya na karba sunansu ne idan an yi su tare da mutane.” Wannan magana na nufin ne ba ya halatta ga wasu mutane su yi tunga, su yi Azumi ko Idi ko layya ba tare da sauran jama’a ba.

 

Lalle ne kowane musulmi ya yi waxannan ibadodi tare da Sarki da sauran jama’a.

 

Ka ga da Allah zai sa masu wa’azi a wannan zamani namu su rungumi wannan aqida, su kuma yayata ta tsakanin musulmi, da kansu ya hadu a cikin gunadar da wannan ibada. Kuma rikitta da rigingimun da ke qamari a tsakanin tsirarun musulmi a qasashen gabasci da yammacin Turai sun faxa. Mafi sauqin hanyar da wannan manufa ke iya tabbata kuwa a hasashena, ita ce kafa wata hukuma ko cibiya mai zaman kanta wadda za ta kula da farawa da qarewar kowane wata kamar yadda Shari’a ta tanada. Ta haka da zarar sun tabbatar da tsayuwar watan Azumi ko qarewarsa, sai su kama Azumi tare su aje tare.

 

Idan kuwa suka neme shi qaura-wambai, amma ganinsa ya faskara, to sai a jira Sha’abana ya cika kwana talatin, sannan a dauki Azumin. Shi kuma Ramalana ya cika talatin xin sannan a aje. Idan kuwa har hakan ta faskara, wato suka kasa ganin watan a garin da suke, to sai su yi aiki da ganin da wani gari na musulmi da ke kusa da su, suka yi masa. Su dauki Azumi tare da su. Iyakar abin da za su iya yi kenan, Allah kuwa ba ya dora wa rayuwa abin da ba ta iya dauka.

 

Wannan mas’ala ta tabbatar da kamawar watan Azumi magana ce babba, da Malamai suka dade suna qoqari a kanta, kuma har yanzu ba su daina ba. A kan haka ina so in jawo hankalinmu bisa wasu al’amurra kamar haka:

 

Ya zama wajibi a kan kowanenmu ya ji tsoron Allah, ya kiyaye tare da tsare alfarmar ibadarsa da ta sauran mutane. Duk wata magana ko fatawa da za mu yi riqo da ita ta wani Malami, to mu tabbata ta dace da abin da nassosan Shari’a suka qunsa. Kada mu riqe su saboda kawai Malamin dan mazhabarmu ne, ko garinmu ko qungiyarmu.

 

Sannan kuma yana da matuqar kyau mu fahimci cewa, matsalar ganin wata, matsala ce da ke lale marhabin da qoqarce- qoqarcen Malamai na Ijtihadi. Kuma babu wanda ya isa ya hana wani daga cikin Malaman yin ban hannun makaho da wani a cikinta. Bai kuma kamata hakan ya zama dalilin gaba da qiyayya da xaixaicewa tsakanin musulmi ba. Domin kuwa babban abin da nassosan Shari’a ke qoqarin tabbatarwa shi ne haxin kan al’umma.

 

Idan hukumar da abin ya shafa ta tabbatar da tsayuwar wata ko da, ta wata hanya mai rauni, to, ba ya kamata wasu ‘yan tsirarun mutane su qi yarda da hukuncin, don yin hakan za ta haifar da wani rikici da rarrabuwar kan jama’a.

 

Babban abin baqin ciki duk bai fi irin yadda wasu mutane ke shafa wa wannan ibada mai girma kashin kaji ba, ta hanyar amfani da ita su riqe wani makahon karatu, suna matsayin masu goyon bayan mutanen wani gari. Kuma su dage kai da fata a kan sai kowa ya bar ganewarsa ya dawo ga tasu, suna yi suna kuma zuba wa ra’ayin nasu rigar Shari’a har da naxa masa rawaninta, ba tare da sun kula da abin da zai haifa wa jama’a xa mai ido ba.Kai! Allah dai ya kiyashe mu, ya kuma taimake mu a kan gane makamar Addini, tare da biyar Sunnar Shugaban Manzanni Sallallahu Alaihi Wasallama sau da qafa.

 

Ya kuma sa mu kasance masu son ganin al’ummar musulmi ta zama tsintsiya madaurinki daya.

 

A taqaice wannan shi ne irin shirin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayinsa na babban Malamin wannan al’umma, kan yi, don fuskantar watan Azumin Ramalana.

 

Kuma haka ya kamata a sami duk wanda ke fatar haduwa da rahamar Allah a gobe qiyama na yi.

 

Domin shi watan Azumi, kamar irin baqon nan ne da ke ciyar da masu masaukinsa. Saukarsa na farkar da gafalalle, ta fadakar da wanda ke farke.

 

Da zarar ya kama ko wane Malami zai qara kuzari da qaimi ga qara jagorancin jama’a zuwa ga bautar Allah, da yin nesa-nesa da su daga ayyukan zunubi da ashsha.

 

Da haka sai wuraren masha’a su koma fanko, masallatai kuwa su cika su batse, alherai su daxa qaruwa, komai ya tafi yadda ake buqata. Allah yasa muna fahimtar karatun

 

Allah ya karbi Ibadun mu na wannan watan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button