RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA UKU (3).
RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA Part (3) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE
1.4 Bayanin Wasu Hukunce- Hukuncen Azumi:
Cewa ANNABI S.A.W nayi wa Sahabbansa bayanin wasu hukunce-hukuncen Azumi, abu ne da ba ya buqatar kafa hujja domin tabbatarsa.
Domin kuwa abubuwan da wannan littafi ya qunsa gaba daya na tabbatar da haka ne.
Iyakar abin da za mu ce a wannan sashe shine, buqatar kawai da ake da ita ga Malamai da masu da’awa a wannan zamani namu, shine su mayar da hankali ga karantar da mutane hukunce-hukuncen na Azumi tun kafin watan nasa ya kama.
Su kuma ci gaba da yin haka a tsawon kwanakinsa. Kowa daga cikinsu ya yi iyakar yinsa, ta hanyar qirqiro salailai da dabaru daban-daban da za su taimaka masu ga tabbatar da wannan guri.
Kai! Yin haka ma kusan wajibi ne domin kuwa jahilci a yau ya yi wa musulmi riga da wando. Kuma masu fadakarwa da wayar wa jama’a da kai a kan al’amurran addini sun qaranta, musamman a cikin ya’ayyuhannasu.
Kai! Ko a cikin ya’auyyuhallazina amanu, abin sai hattara. Su kuwa sauran jama’a musulmi, wadanda ba Malamai ba; mazansu da mata, ba abin da ya kamace su illa su mayar da hankali ga neman sanin makamar hukunce-hukuncen Shari’a wadanda suka shafi ibadodi na yau da kullum, da irin shirin da ya kamata su yi don fuskantar wannan wata na Azumi mai alfarma.
Su lizimci karanta littafai, da sauraren kasakasai, da halartar wuraren wa’azi da tafsirin Alqur’ani. Domin kuwa babu yadda za a yi aikin mutum ya yi kyau face ya qetaro irin wadannan matakai. Yin haka ko shakka babu wajibi ne a kansu, matuqar suna son tsira da wani abu gobe qiyama.
Domin kuwa duk wanda ya aikata wani aiki ba yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a yi shi ba, to, ya yi aikin banza. A duk lokacin da kuma mutum ya dage kai da fata a kan biyar tafarkin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da koyi da shi, a cikin komai nasa, da ya hada da magana da aiki da gargadi, to shi ne mutum na gari wanda kuma ya yi gam da katar. Allah yasa muna fahimtar karatun
Allah ya karbi Ibadun mu na wannan watan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH