Rikicin Siyasa Ne Ya Haɗasu Da Masu Mulki. ~Cewar Farfesa Ibrahim Maqari.

Babban malamin masallacin Abuja kuma shehin Darikar Tijjaniyya a najeriya Sheikh Prof, Ibrahim Maqari Hafizafullah ya rubuta a shafin sa na Facebook.

 

Farfesa Ibrahim Maqari inda ya bayyana ra’ayin sa akan hukunci da kotun shari’ar Musulunci ta yanke wa Malam Abduljabbar Nasiru Kabara a Yau Alhamis 15/12/2022. A birnin Kano. Ga abunda ya rubuta;

 

Mafi yawan waɗanda aka kashe saboda tuhumar zindiƙanci a tarihi idan mai karatu ya zurfafa bincike zai samu rikicin siyasa ne ya haɗasu da masu mulki.

 

Amma ba zindiƙancin ne dalilin kisan ba. Cewar Farfesa Ibrahim Maqari Zaria.

 

A kwanakin baya kuma shehin Malamin ya rubuta cewa Malam Abduljabbar Nasiru Kabara yana da’awar kare Annabi Muhammadu ﷺ ne cikin jahilci, sannan kuma sauraran maganganun sa ka iya raba mutum da Imani, don zantuka ne na zindikanci da fasikanci.

 

~ Cewar Farfesa Ibrahim Maqari Zaria.

 

Muna Addu’an Allah ya kara wa Manzon Allah SAW daraja ya bamu albarkacin sa. Amiin

Share

Back to top button