Rikicin Tsakanin Niger Da ECOWAS Yazo Karshe Malaman Tijjaniyya Sun Magantu A Niger.

RIKICIN TSAKANIN ECOWAS DA SOJOJIN NIJAR YAZO KARSHE.

 

ZIYARA CIKIN HOTUNA: Ziyaran Khadimul Faidah Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi OFR Garin Chota Wurin Khalifa Sheikh Musa Abubukar Chota Dake Kasar Niger.

 

Lamarin Ya Faru Ne Bayan Samun Babban Matsala Tsakanin Kasar Niger Da Kuma Kungiyar ECOWAS Wanda Alh Ahmad Bola Tinubu (Shugaban Najeriya) Yake Jagoranta, Inda Wasu Daga Cikin Manyan Malaman Addinin Musulunci A Nigeria Suka Kai Ziyara Kasar Don Shiga Tsakani.

 

Karo Na Biyu Kenan Da Malaman Addinin Musulunci Suka Ziyarci Kasar Niger Don Kawo Maslaha A Tsakanin Niger Da ECOWAS.

 

Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Yakai Ziyaran Ne Don Tattaunawa Akan Kawo Karshen Rigimar Niger Da ECOWAS. Allah Ya Kawo Mafita. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Babangida A Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button