Riko Da Hakikanin Sunnar Manzon Allah SAW A Wurin Shehu Ibrahim Inyass RA.

Maulana Sheikh Ibrahim Niasse RTA Riƙonsa Da Sunnah.

 

Imam Hassan Cisse RTA Yace: lokacin da akayi Yaƙin Ramadhan (October, 1973 wanda Kasashen Larabawa suka yaƙi Israel kuma suka ci Nasara ƙarƙashin jagorancin Egypt da Syria).

 

Imam Hassan yace, Sai Sheikhu RTA ya umurce ni na Rubuta wasiƙar Taya Murna ga shuwagabannin ƙasashen Larabawa tun balle Sarki Faisal (Sarkin Saudia) da Anwar Sadat (Shugaban Ƙasar Egypt) Domin tayasu murnar Munasaabah guda biyu; Munasabar Nasarar Yaƙi da Munaasabar Idin Ƙaramar Sallah, Allah SWT Ya Kimsa mini Kalmomi Masu Daɗi da ma’anoni wajen rubuta wasiƙar sai dai da nazo karshen wasiƙar dana Rubuta ga Sarki Faisal sai nace:

والاعتماد على الله وبكم

Ma’ana:

Dogaro yana ga Allah da ku

 

Dana kawowa Sheikhu RTA wasiƙun domin ya saka hannu sai ya saka hannu a wasiƙar Anwar Sadat amma banda ta Sarki Faisal sai ya umurce ni dana sake rubuta ta Sarki Faisal kuma na canja wancan Jumlar ta koma:

الاعتماد على الله ثم بكم

Ma’ana:

Dogaro yana ga Allah Sannan daku

 

Dana tambayeshi Dalili sai yacemin za’a iya amfani da yadda ka rubuta sai dai kawai ta saɓa da abunda yazo daga Sunnah kuma ta saɓa da ladabi ga Allah, Saboda bai kamata ayi amfani da Harafin و da yake nuni izuwa ga daidaito tsakanin abu biyu a janibin Allah da bawa ba, sai dai ayi Amfani da Harafin ثم da yake nuna banbanci tsakani Martabobin guda biyu shi yasa Annabi SAW yace:

 

لا تقولوا ما شاء اللهُ وشاء فلانٌ، ولكن قولوا ما شاء اللهُ ثم شاء فلانٌ

Ma’ana:

Kada kuce Abunda Allah Yaso da Abunda Wane Yaso sai dai kuce Abunda Allah yaso Sannan Abunda Wane Yaso.

 

Domin Hakan yana nuna “Nufin” na haƙiƙa daga Allah yake shi kuma “Nufin bawa” kawai yana bin bayan Nufin Allah ne.

 

“Yan uwa wannan shine SHEIKH IBRAHIM NIASSE RTA ƊINMU.

 

Daga: Aliyu Uthman Bashir

Share

Back to top button