Rubutun Al-kur’ani Bugun Hannu Da Ya Kai Shekaru 300 Cif A Jihar Kano

Rubutun Al-kur’ani Bugun Hannu Da Ya Kai Shekaru 300 Cif A Jihar Kano

 

Daga Janaidu Ahmadu Doro

 

An gano wani daɗaɗɗen Alqur’ani mai Girma wanda wani Gwani ya rubuta shekaru dari uku da su ka gabata a jihar Kano.

 

Tsohon kwafi na Alqur’anin da aka samu a kauyen Dambatta, yana daga cikin wadanda Gwani Musa Allah ya ƙara masa yadda ya rubuta a zamaninsa.

 

Kamar yadda bincike ya nuna, rubutun alkur’anin ya kai kimanin shekara dari uku da daya kamar yadda aka ga lissafin da ke shafin bayanai da ke jikin littafin.

 

Allah ya kara daukaka musulunci da Musulmai. Amiin

 

Daga: Jaridar Rariya

Share

Back to top button