Saƙon Sheikh Ɗahiru Bauchi RA Kashi Na Biyu Akan Matsalar Tsaro A Najeriya.

Sabon Sakon Maulanmu Sheikh RTA

 

Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA Ya Sake Bayyana Wani Sako Kamar Haka;

 

Shehu yace wadannan Mutanen sun yi laifi wa Allah, basu Girmama shi ba shiyasa suka fada cikin wannan 6arna, yanzu zamu Koma kan tubawa Allah ya yaye mana wannan Bala’i yai mana maganinsu koda kuwa Gomnati ne Allah yai mana maganin ta. Zamu koma;

 

Istigfari (1,111,000) Sai

 

Ya Ladifu (1,111,000) Sai

 

Hasbunallahu Wani’imal Wakeel (1,111,000) Sai

 

Salatul Fatihi (1,111,000)

 

Dukkansu irin adadi a da aka bayar na Alamtara din kenan, Sa’annan Wanda bai iya Salatul Fatihi ba zaiyi duk Wanda ya iya.

 

Allah ya kawo mana Karshen Kidnapping, Boko Haram, Bandits da Sauransu Albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam

Allah yakarawa Baban mu Lafiya da tsawon rai Albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam A’min

Share

Back to top button