SABANIN FAHIMTA TSAKANIN MALAMAN ADDINI BA MATSALA BACE TO AMMA A INA NE MATSALAR TAKE NE ???.

SABANIN FAHIMTA TSAKANIN MALAMAN ADDINI BA MATSALA BACE TO AMMA A INA NE MATSALAR TAKE NE ???.

 

– Barr. Aminu Balarabe Isa

 

Sabanin fahimta abu ne dake da asali a Da’irar

Islama, tun daga zamanin Manzon Allah S.A.W. Har izuwa zamanin Sahabbai, Tabi’ai, da zamanin Limaman Mazhabobi biyar manya da Muke da su a Musulunci. Misali, Sahabbai sun sa6a wajen fahimtar maganar Manzon Allah S.A.W. Na cewa: “Kar kuyi Sallar la’asar sai kunje (Baniu Queaiza)l. Wasu sukai sallah a hanya, wasu kuma sai da suka je Bani Quraiza bayan faduwar rana, sannan Sukayi Sallar la’asar. Amma Annabi S.A.W. Bai zargi kowa a cikin su ba. Imam Muslim R.A.

 

Sannan Imam Malik R.A. Da sauran Limaman

Mazhabobi sun sassa6a akan hukunce hukunce masu yawa, Amma duk da wannan baisa wani yana kafirta wani ba, ko ya aibatashi ba, haka dai lamarin yaci gaba har izuwa zamani mai tsawon gaske. To shin mu a yau a haka lamarin yake a wajen mu?.

 

A’a lalle ba haka lamarin yake ba, zaka samu

kafirce~kafirce, zage~zage da cin mutuncin juna a tsakanin mabanbanta fahimtar da Muke da shi musamman a Najeriya. Gashi kuma abin duk bai kai tushe ba, a rassa ne kadai abin yake.

 

Gashi kuma Allah S.W.T. Yana cewa: “Kuyi riko da igiyar Allah baki dayanku, kada ku rarraba”. Shin ya lamarin yake? Haka zamu zauna a cikin cin mutuncin juna da tozarta juna har makiyan mu su karasamu?.

 

TO SHIN A INANE MAFITAR TAKE NE?

 

To ‘Yan uwa MAFITAR guda daya ce da masu son zuciya basa son a fada shine kowa yayi iya

fahimtarsa Bisa Ilimi da sanin yakamata, batare da cin mutuncin ‘Yan uwa Musulmai ba ballantana kafirtasu. Sannan mu hada kai da suna daya na musulunci, idan akayi haka za’a samu Nasara. Duk wanda ya sa6a ba Musuluncin gaskiya bane. Domin Manzon Allah S.A.W. Yana cewa: “Musulmi na gaskiya, shine Musulmin da ‘Yan uwansa Musulmai suka Tsira daga Sharrin hannunsa da harshensa”. Imam Muslim R.A. Dan haka dukkan musulmi ya fadaka, fadaka, kuma su/mu farka daga baccin da mukeyi domin mune wanda guguwar zamani tafi biba sosai.

 

Manufata a samu wayewa da Karin fahimta

domin samun hadin kai da fahimtar juna, tsakanin Al’ummar Musulmai, sannan masu 6ata abubuwan sugane suna da asali a cikin Addinin musulunci, ko Dai basuyi Karatu ba,

ko kuma son Zuciya da neman girma da mabiya ne yake hanasu fadar gaskiya, idan kuma rashin sani ne haka, to ya kamata su tashi tsaye su nemi sanin hakan.

 

Idan kuma son Zuciya ne, to fa ba mai bude

Zuciyar da Allah ya Shafe basirar ta, kuma zamu cigaba da wadannan abubuwan gwargwadon hali da fahimtar mu, domin wayar da kai.

 

A shirye muke da mu karbi gyara ko shawara daga ‘Yan uwa Musulmai, ko daga wane bangare mutum yake matukar a kan ilimi ne gyaran yake.

Back to top button