Sahabban Annabi S.A.W Ba Ka Bar Su Ba, Sun ci Addini Sun Hainci Ma’aiki inji Ka, Sai Kai Ne Zaka Gyara.

Dukkanin Shuagabannin Addinin Musulunci Tun Daga Kan Sahabban Manzon Allah S.A.W Babu Wanda Ya Tsira Daga Zagin Ka Da Aibatawar Ka, Da Cin Mutuncin Ka.

 

Sahabban Annabi S.A.W ba ka bar su ba, Sun ci Addini Sun Hainci Ma’aiki inji ka, sai kai ne Za ka Gyara.

 

Tabi’ai, Tabi’ut Tabi’iin duk ba su iya ba, sai kai.

Marawaitan Hadisi, tun daga Ɗabaƙa ta Farko, Su Malik, Imam Ahmad, Bukhari, Muslim, Da Littatafa Na Sihahu, Da Sunan, Da Masaaniid, Duk ka Bi ka zage ka Aibata, ka La’anta, duk Ka Ƙala musu Sharri da Ɓatamci da cin mutunci, duk ba su sa Annabi ba, Maqiyan sa ne, sai kai.

 

Kada Masharhanta su ji Labari, Irinsu Nawawi, Ibnu Hajar, Da Manyan Malaman Siyar Irin su Alƙali Iyad, Duk ba sa san Annabi, Maqiyan sa ne sai kai.

 

Tunda dai Manzo S.A.W Ya ƙaura, Shekara 1400 da Ƴan Kai, Duk Wanda Suka yi wa Addini Hidima na Ilimi da rubuta Hadisai da Sunan, Duk ba Masoyin Annabi a ciki, Sharri da ɓatanci suka rubuta suka ɗora Al’umma akai, kuma tun daga farkon Musulunci zuwa Yau, ba a samu wani Malami Mai ilimi da Ya fahimci haka ba sai kai, kai ne kazo za ka sabunta Addini ka maida shi Yadda Manzo ya Barshi, Saboda babu wanda ya ke son Annabi da zai ba shi Kariya, sannan kuma zai gane cewa duk Littatafan Musulunci ƙarairayi ne na Banu Umayyah, sai kai kaɗai da Ina jin Wani sabon wahayi ne akai ma.

 

To In ba irin Wannan Hukuncin ba, wane Hukunci kake sa rai za ai ma ?

 

Shawara da izina ga Malamai anan Shine:

 

A yi Addini da Wa’azi dan Allah A guji Afkawa Malami Magabata wanda Suka hidimtawa Addini, A sani cewa Wallahi Wallahi Aikin da sukai wa Allah, ba sunyi ne kawai da iya yin kan su ba, Bari dai Allah ya zaɓe su wajen Wannan Aiki, kuma Aikin da suka yi wa Musulunci, da Shine Allah ya yi “Hifzin” nan da ya faɗa na ( إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون) Kuma wallahi Allah ba zai taɓa bari wani ya ci Mutuncin Wanan Bayin Allah ba, ko da gaskiya ko ba gaskiya ….

 

A kiyaye Mutunci Malamai Magabata, Kar a manta ba dan wanan Aikin da sukai ba, wllh da Wannan Musulunci da kake takama da shi bai zo ma ba, da sai dai ka tashi a Bamaguje Ko Mai bautar Tsinburbura.

 

Allah ya kiyashe Mummunan karshe, Shi kuma Mallam AbdulJabbar Ina Fata Masoyan sa su taya shi da addu’a Allah ya sa wanan Hukunci ya Amshe shi hannu biyu a zartar masa da shi, ko ya taƙaita masa na lahira. Amiin

 

Daga: Shehi Mai Jama’a

Share

Back to top button