Sako Zuwa Ga Malam Naziru Sarkin Waka Akan Batun Abulfath Sani Attijany

ZUWA GA MALLAM NAZIRU SARKIN WAKA.

 

Gaskiyane..! Addinin Musulunci bai ginu akan zagi ba, bai ginu akan husuma da kuma taba mutumcin sashe zuwa sashe ba, sannan kuma ba dai-dai bane zagin Jagororin wasu da sauransu, madallah da nasiha kyakkyawa.

 

Amma da naso a babi na adalci Mallam Naziru ya dauko curin zantukan Malaman Izala na shekaru 40+ da suka gabata, sai ya dauko zantukan Mallam Abulfathi da sauransa, ya daurasu a mizani, sannan sai ya nemo amsoshin wadannan tambayoyin.

 

1- Shin shine farau a zagin Malaman nan, ko kuma su wadannan Malaman da kake cewa ya zaga sune suka farar da zagin magabatanmu.

 

2- Shin cikin magada su wadannan Malaman, babu guda da a halin yanzu yake zagin jagororinmu, idan akwai me yasa Mallam Naziru bai yi musu nasiha ba…satar amsa ya bincika zai samu wanda yake zagin dibar albarka ga Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A).

 

Munji mungode da wa’azi, amma ya dace Malamin yake dai-daito da adalci wajen wa’azin nasa, kada ya zamo bangare laifin bangare guda kawai yake kallo, alhali sashe gudan da mai yiwuwa yake karewa sune silar tabarbarewar komai.

 

ALLAH YA BADA IKON WANZAR DA ADALCI.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button