Sako Zuwa Ga Sheikh Ibrahim Maqari Hafizafullah.

Zuwa Ga Mai girma Imam Prof. Ibrahim Ahmad Maqari Hafizafullah.

 

Bayan gaisuwa ta girmamawa da jinjina, ga saƙon da nake son in isar, amma na kasa gane shin a waƙa ya zo, ko a wani abu na daban, ga dai saƙon nan ya Imamaddeen.

 

Imamu da gaskiya aka sanku babu batun riya..

Imamu da ku mutane ke hararo gaskiya..

Imam ai wanga saƙo ya disashe danniya..

 

Faɗa masu gaskiya in sun ji tai masu kariya..

Faɗa masu don isar saƙo da sauke ɗawainiya.

Faɗa masu babu tsoro ko biɗar wata duniya.

 

Faɗa masu malami masani a kogin tazkiya.

Faɗa masu.. jarimi gwarzo “biduni” hayaniya.

Faɗa masu ai faɗin shi ne ya daƙile ‘yan tsiya.

 

Daga: Saleh Kaura

Share

Back to top button