SALATUL IBRAHIMIYYA: Yadda Salatul Ibrahimiyya Ya Kasance Tun Zamanin Manzon Allah SAW.

YADDA SHA’ANIN RUWAYAR SALATIN IBRAHIMIYYA YA KASANCE.

 

Lokacin da Sahabi Bashir Bin Sa’ad ya tambayi MANZON ALLAH (S.A.W) : ALLAH ya umarce mu da mu yi maka Salati, to ta yaya zamu yi ma ka shi? ANNABI (S.A.W) yayi shiru na tsawon lokaci, Maruwaicin yace: Har sai da muka shiga damuwa saboda shirun da yayi, tukunnah daga baya ya karanto Salatin Ibrahimiyya.

 

Misalin yadda abin yake (ANNABI S.A.W madaukakine ga daukar siffa a misali da komai da kowa) amma kamar kai ne kaje gaban Sarkin garinku, sai mai fadi yace da ku: Lallai ku gaisar da wannan Sarki na ku kuma ku jinjina gareshi, sai wani daga cikinku yace da Sarki “Mai Martaba koya mana yadda zamu gaisar da kai kuma mu jinjina maka”, shin aikin mai martaba ne koya muku yadda zaku gaisar da shi kuma ku jinjina masa?

 

To amma saboda saukin hali irin na MANZON ALLAH (S.A.W) da kuma dabi’arsa ta “Tawadi’u” ya sanya ya bashi salati na Ibrahimiyya a irin salon “Kada ku fifita ni akan Yunusa Dan Matta” amma lallai umarnin ALLAH kai tsaye na “KU YI SALATI A GARE SHI” to kofa ce budaddiya na yi masa salati da kowacce siga, muddin babu guluwi, ko illa cikin kalmonin.

 

Domin shi bai hani da hakan ba, Sahabbai sun yi masa salati ta sigogi mabambanta, haka nan Malaman Musulunci su ma sunyi masa da sigogi mabambanta, kuma ALLAH ya karba, kuma sun dace Duniya da lahira.

 

ALLAH KA DATAR DA MU FAHIMTAR NASSI, YADDA YA DACE. AMIIN

 

DAGA: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button