Sallamawa Sheikh Ɗahir Uthman Bauchi RA Wajibi Ne Ga Dukkan Yan Darikar Tijjaniyya Musamman Yan Nigeria.

WAJIBI NE BA RA’AYI BA!

 

Sallamawa Sheikh Ɗahir Uthman Bauchi (Lisanul Faidha) wajibi ne ga dukkan yan ɗarikar tijjaniya musamman yan Nigeria.

 

 

Dalili kuwa Shehu Ibrahim Inyass RTA yace “Karɓar Ɗarikar tijjaniya bata da amfani ga mutum sai ya kasance mai girmama dukkan ya tijjaniya musamman manya daga ciki, wato shehunnai da muqaddamai”

 

 

Shehu Ɗahiru Uthman Bauchi, Shehi ne a ɗariqar Tijjaniya, Khalifan Shehu ibrahim ne wanda Shehu Ibrahim ɗin yayi wa iznin abu biyu kamar haka:

 

 

1. Tsarkake ɗarika: Shehu Ibrahim yana yiwa Shehu Ɗahiru kirarin “Mai tsarki ka tsarkake mana ɗariqar mu”. a wannan zamanin babu dattijo kamar sa wanda ba a isa a taɓa Darikar tijjaniya ba sai yayi tsawa ga kowanene sai Shehu Ɗahiru Uthman Bauchi shi kaɗai.

Yana tsawatarwa idan akayi wani mummunar motsi cikin ɗarikar Tijjaniya.

 

 

2. Harshen halara: Shehu yace duk abinda Shehu Ɗahiru ya faɗi, ni ne na faɗa. Shi kuwa Shehu kun san wanene yake magana a cikin sa. Alhamdulillah har maqiyya Ɗariqar tamu sun shakkar magana dashi saboda tsananin hikima da iya sarrafa zance cikin ilimi.

 

Taron Bauchi ya isheka ka gane akwai sa hannun Allah dumu-dumu cikin lamarin Shehu Ɗahiru Bauchi.

 

 

Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana da mamakon Faidha Bijahi Rasulillah SAW.

 

Mun_Sallama_tun_jiya.

 

Daga_ Sir Sadauki

Founder AREWA YOUTHS ALLIANCE

Share

Back to top button