Salman Rushdie Wanda Ya Yi B@tanci Ga Annabi Ya Rasa Ido Daya Da Hannu Guda.

Salman Rushdie Wanda Ya Yi B@tanci Ga Annabi Ya Rasa Ido Daya Da Hannu Guda,

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache

 

Marubuci Sir Salman Rushdie ya rasa ido daya da hannu guda bayan harin da aka kai masa a birnin New York na Amurka kamar yadda wakilinsa ya shaida wa manema labarai,

 

Har yanzu akwai raunuka kusan 15 a kirjinsa da ba su warke ba, kamar yadda eja dinsa Andrew Wylie mazaunin birnin New York ya shaida wa jaridar El Pais ta Sifaniya harin mummuna ne,

 

Mista Wylie ya kara da cewa ba zai bayyana inda marubucin yake ba an dai kai masa harin ne a lokacin wani taro,

 

Sir Salman ya dade yana fuskantar hare-hare da barazanar mutuwa tun bayan shekarar 1988 kan littafinsa na Ayoyin shaidan mai cike da ce-ce-ku-ce,

 

Yawancin musulmai na kallon littafin a matsayin mai cike da sabo an gurfanar da mutumin da ya kai wa Sir Salman hari gaban kuliya ko da yake ya ki amsa laifin,

Share

Back to top button