Sama da mahalarta Maulidi 150 ne suka nutse bayan kifewar jirgin ruwa a Niger.

A kalla sama da masoya Annabi Muhammadu SAW ne mutane 150 cikin kusan dari 3 da ke kan hanyar zuwa taron Maulidin fiyayyen halitta SAW suka ɓace, bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar Mokwa na jihar Niger.

 

Babban jaridar Daily Trust da ake wallafawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe bakwai 8 da rabi na daren jiya Talata, kuma mafi yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su mata ne da ƙananan yara da suka taso daga garin Mundi duk a jihar Niger.

 

Wasu majiyoyi daga yankin da abin ya faru, sun ce al’ummar yankin sun yi gaggawar kai dauƙi, inda aka samu nasarar kuɓutar da wasu da ransu.

 

Muna addu’an ALLAH ubangiji madaukakin sarki ya jikan wanda suka rasu ya Sadauki da Manzon Allah SAW.

 

Wadanda suke kwance a asibiti Allah ya basu lafiya, ya kiyaye faruwan haka a gaba. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button