Sama Da Mutane Miliyan Uku (3M) Suka Fito Zagayen Mauludi A Garin Zaria Jihar Kaduna.

Al’umma Musulmi sama da miliyan 3 ne suka fito gwanon maulidi a birnin Zariya.
Daga Idris M Usman (Dady Bigja) Zariya.
Yadda miliyoyin Al’ummar Musulmi suka fito cikan su da ƙwarƙwatun su a birnin Zariya Jihar Kaduna domin sabunta gwanon zagayen maulidin Manzon Allah (SAW) a yau Laraba wanda yayi dai-dai da 12 gawatan Rabi’ul Auwal.
“An fara gwanon zagayen maulidin kamar yadda aka saba duk shekara bisani an faro gwanon zagayen maulidin ne tun daga Kofar Kuyanbana har izuwa fadar Maimartaba Sarkin Zazzau Dr. Amb. Ahmad Nuhu Bamalli (CFR).
Bugu da ƙari an samu makarantun islamiyyu da suka fito suna tafe suna rera waƙoƙin yabo na Manzon Allah (SAW), gami da ƙungiyoyi na zakirai, jiga-jigan malaman Ɗariƙun Sufaye, Sha’irai, Gamayyar tawagar ƙungiyar Salati, duka a domin nuna farin cikin su da tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW).
Gwanon tawagar miliyoyin Al’ummar Musulmin anyi lafiya an kuma tashi lafiya kamar yadda aka saba duk shekara wakilan jaridar ALFIJIR HAUSA sun tabbatar mana da haka.
📸 Hoto: Zuhair Ali Ibraheem