Sarkin Musulmai Sa’ad Yayi Kira Na Gaggawa Ga Hukuma Kan Kisan Yan Mauludi, Gwamnati Ta Daina Wasa Da Rayuka.

DA DUMI DUMINSA:

 

Ran Sarkin Musulmai ya Baci inda yayi magana Cikin Fushi game kinsan gilla da aka yiwa Masu Mauludi a Kaduna inda yace Dole A Kamo Waɗanda Suka Saki Bom Kan Masu Mauludi, Kuma A Hukunta Su

 

Inji. Sarkin Musulmai

 

Sarkin Musulmai Sa’ad yayi kira na gaggawa ga hukuma kan Kisan masu Mauludi yace gwamnati ta daina wasa ana kashe rayukan mutane yace lallai wannan karon baza su bari ba, dole ne gwamnati ta fito ta kama duk wani mai hannu a kisan ta gurfanar da shi a yanke masa babba hukunci daidai da abinda ya aikata.

 

Sarkin Musulmai ya Bayyana cewa haka shekarun baya ma jama’arsu sun fito Zikirin Juma’a aka taresu aka yanka su, gashi yanzu ma an jefawa wasu Bom Dan haka baza su bari ba-Inji Sarkin Musulmai

 

Daga karshe Sarkin Musulmai ya mika ta’aziyarsa zuwa ga iyalai wayenda abun ya shafa, tare da kira ga al’umma da su kwantar da hankalin su Lallai baza’a bari ba za’a dauki kwakkwaran mataki.

 

©Nigeria Reporters Hausa

Share

Back to top button