Sayyada Fatimah al-Zahra da Sayyadi Aliyu RA sun kasance ma’aurata masu kaunar junan su.

Rigar Sayyida Fatimah al-Zahra AS

 

Sayyada Fatimah al-Zahra da Sayyadi Aliyu RA sun kasance ma’aurata masu kaunar junan su.

 

Ko zamu iya tuna yanayin gidan su yake? Yaya suka rayu? Sun yi rayuwa mai sauƙi. Ita ce sarauniyar Aljannah kuma shi ne Zakin Allah, duk da haka basu da abinci a gidansu. Kuma ba su mallaki duniya da yawa ba. Sun shafe kwanaki suna jin yunwa. Sun kwashe kwanaki suna fama.

 

Sun kwashe kwanaki suna gwagwarmaya. Babu wani abinci a gidan su mai kayatarwa. Babu kujera mai tsada da kayan daki masu tsada. Sai ruku’u da sujjada da addu’o’i da hawaye da tsantsar soyayya.

 

Don haka duniya ba wurin zama bale, muyi kokarin bautawa Allah Ubangiji mu don samu yarda a gare shi tare da bin tafarkin Annabi ﷺ

 

Allah ya bamu albarkacin su. Amiin

 

Daga: Babangida A. Maina

Share

Back to top button