Sayyiduna Abubakar (R.A) Yana Cewa;”KU GIRMAMA ANNABI MUHAMMADU CIKIN LAMARIN IYALAN GIDANSA

ANNABI(S.A.W) MASOYIN AL’UMMARSA!

 

*. A CIKIN ALJANNAH: Su Ma ‘Yan Aljannah Bayan Cewa; Sun Shiga Aljannar Ne Da Alfarmarsa, To Zai Nemi Wata Alfarmar a Wajen ALLAH, Za’a Yi Masa Izini. ALLAH Zai ‘Kara Ma Kowannensu Matsayi Akan Matsayin Da Yake Da Shi, Da Albarkar ANNABI MUHAMMADU (S.A.W).

 

Tambaya Anan Ita Ce: Bayan Imani Da Shi Da Kuma Biyayya Ga Abin Da Ya Zo Da Shi, Wanne Abu Zamu Yi Mu Biyashi???

 

Amsa Ita Ce: BABU. To Amma ALLAH Ya Ce Masa;”KA CE MUSU BA NA TAMBAYARKU WANI LADA AKANSA (WATO ABIN DA NA ZO MUKU DASHI) SAI DAI(KU YI) SOYAYYA GA MAKUSANTAN SA”.

 

Su Waye Makusantansa??? Sune Iyalan Gidansa. Kamar Yadda Ya Zo a Cikin Hadisi.

 

Sayyiduna Abubakrin(R.A) Yana Cewa;”KU GIRMAMA ANNABI MUHAMMADU CIKIN LAMARIN IYALAN GIDANSA(Wato Ku Girmamasu Ku Kyautata Musu Domin Soyayyar Da Kuke Yi Masa)”.

 

Tabbas ANNABI(S.A.W) Yayi Mana Soyayya Da Kulawa Wacce Ta Zarce Irin Ta Sauran Manzanni Da Al’ummominsu.

 

Ya ALLAH! Yi Salati Da Taslimi Gare SHI Da Iyalan Gidansa Masu Alfarma, Da Sahabbansa Masu Albarka, Da Dukkan Salihan Bayinka Har Zuwa Ranar Sakamako.

 

ALLAH YA ‘KARA MANA SON SAYYIDUL-WUJUDI(S.A.W) AMEEEEEEEN.

Share

Back to top button