Shahararren Malamin Musulunci Kuma Shehin Tijjaniyya Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare Bari Kano.

Sheikh Tijjani Usman Zangon bare-bari Wani Shahararren Malamin Tafsiri ne a Kano, yana daga cikin shehunan Darikar Tijjaniya A fadin Africa yayi rayuwa ne daga 1914 zuwa 1970.

 

Yayi Shekaru 56 a Duniya Cikin Dan Takaitaccen Lokaci, ya Bayar da Gagarumar gudunmawa a harkar Ilmin Nahwu, Lugga, Sira, Fiqhu, da Tafsir.

 

Yana Cikin Mutanen Farko da Suka Fara Sallah a Fadan Vatican Na Pope Rome A kasar Italy Lokacin Da Suka Je Kiran Su Zuwa Ga Musulunci Tare Da Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq.

 

Allah Ya Jikansa Da Rahma. Allah Ya Sadashi Da Manzon Allah Annabi ﷺ. Ameen.

 

Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button