SHARHI: Wajibi Ne Idan Muna Bukatan Cigaba Mai Daurewa Mu Hada Kammu Tijjanawa.

WANNAN DIN BULALIYACE GAREMU, DA YA DACE MU FARKA, FARKAWA NA GASKIYA DA GASKIYA.

 

A wasu ‘yan shekaru da suka gabata, ya taba dauko wani yunkuri na kokarin zaburar da ‘yan uwa (Tijjanawa) akan samun hanyoyin da za’a bi wajen amfani da yawan da muke dashi a figure, wajen kokarin samawa kawunanmu Makarantu, Asibittoci, Gidajen Marayu, Masallatai, D.s.

 

Amma sai ya zamo bayan zama a tashi, kusan babu guda da yake sake wai-waitar a wanne hali ake ciki. Domin dayawa gani suke hakan ba abune mai yiwuwa ba, a yayin da wasu kuma ke ganin abune mai matukar wahala iya cimma hakan, tun daga wannan lokaci ya tsinke alaqa irin wannan yunkuri, ya dawo zuwa ga fuskantar abinda zai iyayi gwargwadon kokarinsa, kuma sai ya jibantar da al’amarinsa zuwa ga ALLAH.

 

Daga wancan lokaci zuwa yanzu, basu kai shekaru 13 ba, amma sai gashi a matakinsa na shi 1, ya kusan cimma nasarar da ke cikin mafarkinsa saboda ” IDAN HIMMA TA HADU DA JAJIRCEWA, TO BABU NASARAR DA BA ZA’A TA KA BA”.

 

Lallai wannan nasarace mabayyaniya a gareshi da mu baki daya, amma a hakika bulaliyace zazzafa ga dukkaninmu, idan har mutum guda cikinmu zai iya himmar da zai iya samar da irin wannan nasarori a garuruwa mabambanta, to yaya abin zai kasance idan da ace kashi 50% cikin al’ummarmu zasu iya farkawa, su iya tsara taswirar hanyoyin da zasu bi, wajen samar da hakan.

 

ALLAH YA KARA TSAWAITA MANA RAYUWAR WANNAN GWARZO DA YAKE TATTARE DA DIMBIN ALKAIRAI, YA BAMU IKON DAUKAR DARUSSA CIKIN HIMMA DA JAJIRCEEARSA.

 

Daga Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button