Shariff Almuhajir Malami A Jami’ar Yobe Ya Aika Da Muhimmin Sako Ga Kungiyar MSSN.

SAKO NA MUSAMMAN GA KUNGIYAR MSSN:

 

Daga Alkalamin Dr Sheriff Almuhajir

 

Lura ga abunda ke faruwa na wulakanci da kaskanci da wasu dalibai da suke amfani da sunan kungiyar MSSN suke yi ga dalibai yan dariqar Tijjaniyya a wasu jami’o’in Najeriya, misalin irin abunda ya faru a jami’ar BUK da kumwa wani video dake yadawa cewa daga jami’ar Maiduguri ya ke, da kuma shiru da jagorancin MSSN ta Najeriya ta yi akan haka;

 

Mu mun san MSSN kungiyar dalibai ce ba ta da alaka da akidah, dukkan wani dalibi memba ne kuma yana biyan kudin ci gaban MSSN saboda haka, ina kira ga abubuwa kamar haka:

 

1- Ko kungiyar MSSN ta fito ta bayyana matsayin ta akan abunda ke faruwa, shin da izinin ta ake yi ko kuma wasu ke amfani da sunan ta

 

2- Ta sake jaddada matsayar ta akan rashin biyayya ga kowacce akidah

 

3- ko kuma kar kowanne dalibi dan darika ya sake biya, ko zuwa taro, ko kuma shiga cikin ayyukan MSSN, in ko ya je to duk abunda aka yi ma shi ba laifi tunda kowa ya san matsayin su.

 

Ina ganin hakan ya fi alheri da biye musu har wata rana ya zama wata fitinar daban

Share

Back to top button