Shehu Ibrahim Inyass da irin Gudunmawar Daya Bayar Naci Gaban Musulunci a Duniya.

SHEHU IBRAHIM INYASS YA TAIMAKI MUSULUNCI DA KAYAN ZAMANI

Jama’a assalaumu alaikum, har yanzu dai darasin namu zai ci gaba da tarihin wannan Babban Bawan Allah, Shehu Ibrahim Inyass da irin gudunmawar da ya bayar na ci gaban Musulunci a duniya.

Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, Shehu ya koyar da Sunnar Annabi (SAW) ta tsayar da gemu (tsaka-tsaki) irin yadda Annabi (SAW) yake yi. Ya tilasta wa almajiransa tsayar da gemu har aka san su da shi (gemun) wanda a cikin Malikancin Afirka ba a tsayar da gemu. Hakazalika, ya koyar da almajiransa su riƙa karanta Hadisai musamman Bukhari saboda idan ya kawo musu hukunci kan wani abu su san a ina ya ɗauko musu. Amma a da ba haka ake ba, sai dai a riƙa karanta furu’a (littafan fiƙhu), idan za a faɗi zancen Hadisi; sai dai ka ce leƙa cikin muɗawwalatu za ka gani. Muɗawwalatu a nan suna nufin Hadisai. Ta ɓangaren Ayar Alƙur’ani kuwa, da an ɗan faɗi gutseranta sai a ce karanci ayar da tsawonta ka ji.

Alherin da Shehin ya koyar a duniyar Musulunci ba su tsaya nan ba.

Shehu Ibrahim ya hori almajiransa da su dinga yin saukar Alƙur’ani a cikin Sallar Tarawihi lokacin Azumin Ramadhan. A wajen almajiran Shehu aka fara ganin haka a Kaulakha. Sannan ya ƙarfafa yin haddar Alƙur’ani mai girma. Albarkar Shehu da kafa makarantun da ya yi, an samu sauƙi sosai wajen yin haddar Alƙur’ani. Bayan haka, Shehu (RA) ya koya mana ‘yancin zaɓi a cikin addini ta yadda kowa zai bi hanyar da yake ganin zai tsira.

Ɓangaren amfani da kayan zamani a addini

Shehu Ibrahim (RA) ya taimaki addini da kayan zamaninsa da ya tarar wanda Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da su. Shi ne farkon Musulmin da ya yi haka. Ya yi amfani da Rediyo, da Tarho, da Rikoda, da Kamara wajen isar da saƙon Musulunci. Don har yau, akwai gidahumin musulmin da yake ganin yin hoto kafirci ne, amma Shehu Ibrahim ne ya wayar mana da kai a kan amfani da waɗannan kayan a cikin addininmu na Musulunci. Haka nan amfani da motoci da jirgin sama, da lasifiƙa, da agogo, da zuwa asibitoci.

Shehu Ibrahim yana daga cikin waɗanda ya tilasta wa almajiransa zuwa asibiti wanda a da ba a yarda da hakan ba. Sannan ya koyar da yin karatu irin wannan da ake yi na zamani a makarantu.

Shehu Ibrahim (RA) shi ne farkon Musulmi kuma Malami da ya waye ya san cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne. Shi ne farkon malamin da ya yarda cewa Turawa sun je duniyar wata a shekarar 1969 (combo apolo 11) har ma ya yi littafi a kan wannan. Kuma ya yi wa shugaban Amurka na lokacin wasiƙa a kan wannan (documents suna nan a kan haka). Su Malaman Saudiyya cewa suka yi ma duk wanda ya yarda cewa an je duniyar watan kafiri ne, su kuma na Azahar (Misra) suka ce sam ma ba zai yiwu ba. Amma Shehu Ibrahim ne ya gamsar da su (da hujja) har suka yarda da abin.

Shehu Ibrahim (RA) ya kewaya ƙasashen duniya har Chana, Beijin, Honkon, da sauran sassan ƙarshen Asiya don taimakon Musulunci. Ya haɗa kan Musulmi Larabawa da Baƙar Fata. Yana da kishi na haƙiƙa a kan addininsa na Musulunci mai tsafta ba na ta’addanci ba.

Shehu Ibrahim (RA) yana da kishi a kan Afirka. Ya yi tsayuwar daka tare da ba da gudummawa ga samun ‘yancin duk wata ƙasa ta Afirka ciki har da ƙasarmu Nijeriya. Yana da kishin mutane baƙar fata ‘yan’uwansa.

Shehu Ibrahim (RA) ne gwarzon namijin da ya tsaya shi kaɗai ya kori Isra’ila daga ƙasarsa Senigal wanda nan ne hanyar shigowa Afirka. A lokacin, Faransa ta yi wa Yahudawa izinin shiga Afirka ta Senigal ba tare da takardar biza ba ma. Ba domin Shehu Ibrahim ya kore su ba da mu ma yanzu abin da yake samun Palasɗinawa ya same mu. Jamilu Arif, wani ɗanjarida na ƙasar Misra ya faɗi wannan.

Da yake duniya ta bunƙasa da kakkafa ƙungiyoyi don cimma abubuwa da dama da aka tasa a gaba, Shehu Ibrahim ya ba da gudummawa ta wannan fuskar don ci gaban Musulunci.

Shehu (RA) ya ba da gagarumar gudummawa wajen kafa Rabiɗa ta Malaman Musulunci na Duniya (duk akwai hujjoji a kai a hannu). Sannan ya kafa haɗin kan Afirka wanda ta hannunsa ne shugabannin Afirka suka karɓi wannan. Ya kuma kafa ƙungiyoyin da za su taimaki addini irin su Ansarid Dini tare da umurtar almajiransa su kafa.

Manyan ‘yan jarida na duniya Turawa da Larabawa da sauran su duk sun yi magana a kan Shehu Ibrahim (RA). Ustazu Abdulkareemin Niyazi ya yi magana a kan Shehu da irin ƙoƙarinsa a Jaridar Saudiyya. Haka nan Jamilu Arif na Misra ya yi magana a kan Shehu. Sannan babban malamin Saudiyya Sheikh Muhammad Mahmud Sauwaf a cikin littafin da ya yi mai suna “Yawona Zuwa ƙasashen Musulunci” ya yi magana a kan Shehu (RA).

Shehu Ibrahim ne malami baƙar fata da ya samu ɗaukakar yi wa Musulmi Sallar Jumma’a a Jami’ar Az’har ta Misra a 1961, wanda kafin shi ba a taɓa yin wannan ba (RA). Haka nan ya riƙe muƙamai da yawa a duniya. Shehu ne na Musulunci wanda yake da fahimtoci a cikin Tauhidi, ya warware abubuwan da ya gagari malamai a cikin Tauhidi cikin sauƙi.

Daga cikin muƙaman da ya riƙe a duniya akwai shugaban haɗin kan Jami’ar ƙairawani da Jami’ar Az’har. Sannan ya riƙe mataimakin taron Musulunci da aka yi a Karachi ta Pakistan. Yana daga cikin kwamitin da ya kafa Rabiɗa ta Malaman Musulunci na duniya a Makka. Sannan yana cikin kwamitin da ya haɗa kan jami’o’in Musulunci na duniya a Ribaɗ na Moroko. Haka nan yana daga cikin babban kwamitin malamai masu yi wa abubuwa hukunci a Musulunci na Misra. Ya riƙe babban matsayi a taron shekara-shekara na bincike a cikin Musulunci a Misra. Har ila yau, yana da matsayi babba a Majalisar Musulunci ta Jaza’ir da sauran su da dama.

Shehu Ibrahim (RA) ya ci nasara wajen yin kira zuwa shiga addinin Musulunci da hikima da wa’azi mai kyau da jayayya mafi kyau. Idan muka ce Musulunci ma’ana ya haɗa da Musuluncin, da Imani da Ihsani kamar yadda Hadisin Annabi (SAW) ya faɗa a Hadisin Jibrilu. Ba a dinga ɗaukar ɓangaren Fiƙhun addini kaɗai a bar sauran ba kamar yadda ta ke faruwa a wannan zamanin, sai mutum ya haɗa duk gaba ɗaya. Amma idan mutum ba zai iya haɗawa ba, ya tsaya wa Fiƙhun addini na maƙamul Islam ɗin kawai amma kuma ya san cewa akwai karatun Imani na ilmud Tauhidi ba adadi a gabansa da bai sani ba, ballantana kuma ilmut Tasawwuf na Ihsani.

Babban makamin Shehu Ibrahim (RT) na wannan aikin shi ne tsoron Allah, da ilimi sannan ya fahimci zamaninsa (wannan nuƙuɗa ce babba). A taƙaice dai kowa ya tabbatar ba a taɓa yin Gwarzon Namiji a Musulunci ba irin Shehu Ibrahim (RA) a ƙarne na 20, ba mu Afirka ba har da ƙasashen Larabawa.

Ya bunƙasa ilimin addini da Luggar Larabci a Afirka wanda duk ga ‘yan jami’a nan suna ta amfani da karatuttukansa. Bayan wannan, ya watsa ‘ya’ya da jikokinsa da almajiransa a ƙasashen Turai suna musuluntar da su tare da karantar da su. Tun komawarsa ga Allah har yau; har abada duk wani abu mai amfani za ka ga imma dai ‘ya’yansa ko jikoki ko almajiransa ne suke jagoranci a kai.

Shehu ya kafa alheri, ya yaɗa alherin amma sai aka zo da kishiyarsa, zuwa da kishiyoyin abubuwan da ya kafa ne ya kai Afirka cikin bala’in da ake ciki.

Rikicin waɗanda ba su fahimci Shehu Ibrahim Inyass ba kawai ya ta’allaƙa ne a kan ƙin tsayawa a matakin ilimin da suke da shi, inda suke kutsawa cikin fannoni ko matakan addini da ba su san komai a kai ba, “suna matakin Fiƙhun Musulunci amma sai su riƙa tsallakawa Matakin Imani na Tauhidi ko Ihsani na Sufanci su riƙa cewa “ya faɗi kaza a wuri kaza” alhali ba su da ilimi a kai ƙwarai da gaske.

Da kowa zai yi adalci ya tsaya a fanninsa sannan ya ɗauki karatun da Shehu Ibrahim ya yi a kan wannan fannin, da ya san Shehu Ibrahim Shehinsa ne don ya karantar da shi a fannin nasa ma.

Haka nan Shehu Ibrahim ya kawar mana da ƙabilanci a tsakaninmu tare da yauƙaƙa zumunci na ‘yan’uwantaka wanda hatta maƙiyinsa ma ya yi masa shaida a kan wannan. Ko a kan haka, ya dace ƙwarai da gaske mu riƙa yin Mauludin Shehu Ibrahim (RA).

Allah ya saka masa da alkhairi.SHEHU IBRAHIM INYASS YA TAIMAKI MUSULUNCI DA KAYAN ZAMANI

Allah ya saka masa da alkhairi. Amiiiin

Sheikh isma’ila umar almaddah r.a.

Sabi’u Hashim Hassan Al-tijany

Sheikh khaleell zawiyyah Bauchi

Asabar-25/11/2023

Share

Back to top button