Sheik Ibrahim Inyass yace; Amma ni bazan taba ganin Musulmi Mai sunan Manzon Allah SAW ba (wato Amadou Lamine-Guèye) na kyaleshi na zabi Kafiri ba,

SIYASA DA TARIQA

 

A 1960 lokacin da aka fara Siyasa A senegal Léopold Sédar Senghor Ya fito yana neman Shugabancin Qasa, Shima lokacin Amadou Lamine-Guèye Ya fito yana Neman Shugabancin Qasar.

 

Kamar yadda Al’adar Siyasa take kowa Ya ringa tallata dan Takararsa kuma koya yakeso yace ra’ayinsa daya yake Dana Sheikh Ibrahim Niasse RTA, Har Abun yaso ya zama Rigima tsakanin Muridai.

 

Da Sheikhu RTA Yaji Labari sai yasa aka Tara Muridai a masallaci sannan yace musu naji rikici yana so ya balle tsakaninku, Tsakanin wanda suke son Senghor da Lamine kowa yana danganta dan takararsa dani Toh ina so na gayamuku Abunda yake Tsakanina daku shine wannan (Sai Sheikhu Ya ’Daga Carbinsa Sama ya nuna musu). Ma’ana Tariqa ce kawai tsakanina daku.

 

Sheikhu ya cigaba da cewa “Amma ni bazan taba ganin Musulmi Mai sunan Manzon Allah SAW ba (wato Amadou Lamine-Guèye) na kyaleshi na zabi Kafiri ba, Amma duk da haka Ban hana kowa ya zabi wanda yake so ba.”

Naji wannan Qissar wajen Sheikha Bilqees Niasse RTAnha 2015

 

ABUN LURA

1-Wannan yana nuna mana Shehi bashi da iko ya takurawa Muridi wani dan takara.

2-Haka zalika zamu fahimci cewa tariqa daban siyasa daban.

3-Kamar yadda zamu fahimci wajibin Shehunnai ne su fito su hana muridai samun sabanin tsakaninsu.

 

Daga: Aliyu Uthman Bashir.

Share

Back to top button