SHEIKH ABDULKADIR ZARIYA: MALAMIN DA YADA ADDININ MUSULUNCI A KASAR NUPE.
SHEIKH ABDULKADIR ZARIYA: MALAMIN DA YADA ADDININ MUSULUNCI A KASAR NUPE
….Kuma Daya Daga Cikin Manyan Malaman SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI Da SHEIKH ABUBAKAR CHOTA.
A Tarihi Babu Mutumin Da Ya Yada Ilimin Addinin Musulunci Wa Kabilar NUPE Kamar SHEIKH ABDULKADIR ZARIA ANNUPAWAIY
An Haifi SHEIKH ABDULKADIR ZARIA A Garin AGAIE NIGER STATE A Shekarar (1909) Ya Taso A Gidan Karatu Ne Domin Mahaifinsa Malami Ne Mai Karantarwa A Makarantar Allo Da Kuma ZAURE.
Bayan Ya Girma ALLAH Yasa Mishi Son Yin Karatun Ilimi Hakan Ya Tursasa Mishi Barin Mahaifarsa, Garin AGAIE Zuwa Kasashen Hausa Dan Neman Ilimi
Bayan Ya Zama Teku A Fannonin Ilimin Addinin MUSULINCI Kama Daga FIQHU, NAHWU, BALAGA, SARFU, LUGGA, MANDIK, ALQUR’ANI Mai Girma Da Kuma Hadisai da TAUHIDI
Sannan Sai Ya zo ZARIA Inda Ya Kara Karatun Kuma ALLAH Ya Nufe Shi Da Zama A Garin ZARIA Inda Ya Kafa Babbar Jami’arsa Ta Ilimin Addinin MUSULUNCI A ANGUWAN LIMANCIN IYA, Dalibai Daga Fadin NIGERIA Da Kasashen Ketare Sukai Ta Tururuwar Zuwa Neman Ilimi A Wannan Jami’ar ta sa Wanda Har Yanzu A Bada Karatu Kamar Da.
Daga Nan Sai SHEIKH ABDULKADIR Ya Koma Garin AGAIE Inda Yake Zuwa LOKACI Bayan LOKACI Yayi Jihadi Ya Rabasu Da Wasu Muna Nan Al’adu Na Jahilci Da Suke Aikatawa Kamar Rashin Kullen Mata Da Rashin Riko Da Addini Da Tsafi, Ya Kuma Yada Ilimin ADDINI A Cikin AL’UMMAR NUPE
SHEIKH ABDULQADIR Ya Shiga Kauyuka Da Birane Kwararo Kwararo Na Nufawa Tsakanin Jihar NIGER Da Kwara Da Kogi Yana Shiryar Da Su Bin Tafarkin ADDININ MUSULINCI A Sanadiyyar SHEIKH ABDULQADIR Dubannin Nufawa Sun Zamo Manyan Malamai Yanzu Dai Zai Yi wuya Ka Samu Wani Malami Ba Nupe A Yankin Neja da Kwara da Kogi wanda a karatunsa bai da Alaqa Da SHEIKH ABDULKADIR Ba Iya Nan Ba Kusan A Fadin Kasar Mu NIGERIA Babu Jihar Da Bai Da ALMAJIRIN da ya koyar ilimi.
Yana Daya Daga Cikin Malaman Da Suka Sallamawa SHEIKH IBRAHIM INYASS RTA. SHEIKH ABDULQADIR Shine Sanadiyyar Zuwan SHEIKH IBRAHIM Zaria Dake Jihar Kaduna.
Bayan Karfafa Darikar TIJJANIYYA A Yankin Nufawa, Shi Ya kai Faidar SHEIKH IBRAHIM INYASS Yankin Wanda Yanzu Za’a Iya Samun NUFAWA Sama Da MILLOON Wadan Da Suke Danganta Kansu Da Faidar SHEIKH IBRAHIM Sanadiyyar SHEIKH ABDULQADIR ZARIA ANNUFAWIY.
Ya Wallafa Littafai Da Dama A Fannonin Ilimi Kamar FIQHU Da Ya bon ANNABI S.A.W Da Fannin Ilimin ALQUR’ANI Mai Girma Da Sufanci
SHEIKH ABDULQADIR Yayi Wafati A Shekarar (1980) Wanda Suka Gaje Shi Bayan Wafatin Sa Daga Cikin Almajiransa Akwai “Ya”yansa Kamar Haka:
Marigayi SHEIKH TIJJANI KHALIFA Da
SHEIKH MALAM SANI KHALIFA (Mataimakin Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Ta Kasa).
Daga Cin ALMAJIRAI Akwai
Sheikh Idris Fogun Bida
Sheikh M. Nasiru Sheikh Abdulkadir Zaria
Sheikh Fadalu Gwargwaje
Sheikh M. Magaji Banufe
Sheikh M. Idi Kaura
Sheikh M. Sani Dandume
Daga Cikin Almajiransa Wanda Sukayi Fice A Duniya
SHEIKH DAHIRU USMAN Bauchi,
Wanda Yayi Karatun MA’ARIFA Da Azkarul Tarbiyya Awajen SHEIKH ABDULQADIR ZARIA.
Da SHEIKH ABUBAKAR CHIOTA RTA.
Daga Rayyahi Sani Khalifa