Sheikh Abubukar Chota Babban Malamin Musulunci Kuma Shehin Tijjaniyya A Kasar Niger.

Sheikh Abubukar Chota an haifeshi a garin Chota dake birnin Yemai a jamhuriyar Niger, a shekara ta 1332 wanda yayi dai-dai da 1914.

 

Sheikh Abubukar Chota ya fara karatun a wurin mahaifin sa daga baya ya shigo birnin Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya. Yayi karatu mai zurfi a wurin Sheikh abdulqadir Zaria, Sheikh Na’iya Zaria da wasu manyan malamai a garin.

 

Ya hadu da Sheikh Ibrahim Inyass, inda ya ziyarce shi kuma Shehu ya bashi yar’sa Sayyada Ummul Khairi, kuma Allah ya azurta sure da samun zuriya masu akbarka.

 

Sheikh Abubukar Chota ya karantar da dukkan mutane ilmin addinin Musulunci dama na Sufanci tare da bada gudumawa sosai don tabbatar da yaduwar Musulunci a yankin Niger, Benin, Togo, Mali, Burkina Faso, Nigeria da sauran su tare da samun babban zawiyar a garin sa na Chota da makarantun addini.

 

Yayi wafati yana da shekara 90 a duniya ranar 28/04/2004, anyi masa makwanci kusa da masallacin sa dake garin Chota. Alhamdulillah na samu damar ziyaran sa da addu’an a gare shi. Allah ya kwautata namu.

 

Allah ya jaddada rahma a gare shi, ya kara masa kusanci da Manzon Allah SAW, ya bamu albarkacin waliyai baki daya. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Babangida A. Maina

Founder Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button