Sheikh Afif Mohammed Taj Shahararren Matashin Malamin Qur’ani Dake Kasar Sudan

Alkur’ani Mai Girma Akwai Dadi.

 

Shaikh Afif Mohammed TaJ matashin malamin Qur’ani ne. Yanzu shine ƙira’arsa ta fi yawo tsakanin Facebook Reels, Instagram da TikTok. Mutane har hawa muryarshi suke yi, suna kwaikwaya. Alamar dai ya karɓu wajen jama’a.

 

Shekaru 3 da suka wuce ba shi ake “yayi” ba. Shaikh Noreen Muhammad Sadiq ake yayi. Wannan makarancin da ya rasu a hatsarin mota a watan Nuwamban 2020. Allah Ya mishi rahama, amin.

 

Su biyun duk ƴan ƙasar Sudan ne. Sun rayu zamani ɗaya. Muryoyinsu sun samu karɓuwa wajen mutane masu yawa. Amma ɗaya bai bayyana ba sai da ɗayan ya rasu.

 

Tsarki Ya tabbata ga Allah wanda yake ɗaukaka sunan bawansa a lokacin da ya so, kuma yake sauke shi a lokacin da ya so. Allah Buwayi gagara misali.

 

اللهم ارحمنا بالقرآن واجعله لنا إماما ونورا وهدى ورحمة، اللهم ذكرنا منه ما نسينا وعلمنا منه ما جهلنا وارزقنا تلاوته آناء الليل وأطراف النهار 🤲

 

– Ibrahiym A El-Caleel.

Share

Back to top button