Sheikh Ahmadu Tijjani Bai Lamunci Shan Taba Ba, Yaushe Wani Zai Zuƙi Wiwi Yace Shi Almajirinsa Ne

Shehin da bai lamunci shan taba ba yaushe wani zai zuƙi wiwi ya ce shi almajirinsa ne

 

Shehin Da Ya Zaɓi Ibada Da Nema Ilimi Fiye Da Sunnar Aure Yaushe Almajirinsa Zai Yi Zina.

 

Shehin Da Ya Haddace Alqur’ani Yana Ɗan Shekara Bakwai Kuma Ya Faɗa Duniya Ya Nemi Sauran Illimmai Tun Da Kuruciyarsa Yaushe Ne Almajirinsa Zai Ce Ya Gama Neman Ilimi.

 

Shehin Da Baya Sallah Sai Cikin Jam’i Akan Lokaci Yaushe Almajirinsa Zai Ce An Dauke Masa Sallah.

 

Shehin Da Ya Ce Maka Ka Bi Umarninsa Cikin Umanin Allah Da Ma’aiki Salawatullahi Wasalamuhu Alayhi In Ka Ga Ya Saɓa Ka Barshi Yaushe Almajirinsa Ya Koyi Wasa Da Hakkin Allah.

 

Manufata Ka Gane Masu Shisshigi Da Barna Da Sunnan Yan Tijjaniyya Ko Alama Ba Su yi Tare Da Shehu Tijjani (RTA).

 

Allah Ya Bamu Lafiya Da Zaman lafiya Albarkar Shehu Tijjani. Amiin

Share

Back to top button